Ana Shirin Kafa Ƴan Sandan Jihohi, Tinubu Ya Ware N140bn ga Ɓangaren Ƴan Sanda

Ana Shirin Kafa Ƴan Sandan Jihohi, Tinubu Ya Ware N140bn ga Ɓangaren Ƴan Sanda

  • Majalisar NEC ta amince da ƙarin Naira biliyan 130 domin gyara da inganta cibiyoyin horas da jami’an ’yan sanda a faɗin Najeriya
  • Sabon tallafin ya kai kuɗin shirin zuwa Naira biliyan 230, yayin da gwamnati ke shirin ɗaukar sababbin jami’an ’yan sanda 50,000
  • Majalisar ta kuma amince da ayyukan raya ƙasa biyu da Bankin Duniya zai tallafa wa da dala biliyan 850 domin inganta rayuwar ’yan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja – Majalisar Tattalin Arzikin Ƙasa (NEC) ta amince da ƙarin Naira biliyan 130 domin gyara da inganta cibiyoyin horas da jami’an ’yan sanda a faɗin Najeriya.

Wannan ƙarin kuɗi ya kawo jimillar kuɗin da aka ware wa shirin zuwa Naira biliyan 230, yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen ɗaukar sababbin jami’an ’yan sanda 50,000.

Kara karanta wannan

Kamfanin Maggi ya kaddamar da sababbin jakadu a Najeriya

Gwamnati ta ware N140bn ga bangaren yan sanda
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima yayin taron kwamitin tattalin arziki. Hoto: @stanleynkwocha/X.
Source: Facebook

Hakan na cikin wata sanarwa da Stanley Nkwocha, a ofishin mataimakin shugaban ƙasa, ya fitar a X a yau Litinin.

Yarjejeniyar da aka cimma

An cimma matsayar ne bayan rahoton kwamitin musamman na NEC kan gyaran cibiyoyin horas da ’yan sanda.

Kwamitin ya bayyana cewa ana gudanar da ayyukan gyara a wurare 13 a faɗin ƙasar, inda aka kammala kashi 30 cikin 100 na ayyukan.

Tun da farko, majalisar ta amince da ware Naira biliyan 100 ga shirin bayan kafa kwamitin a watan Oktoban 2025, bisa shawarar Shugaba Bola Tinubu.

Sanarwar ta ce za a inganta wuraren horaswa tare da ƙarfafa ƙarfin cibiyoyin domin su iya karɓar ƙarin waɗanda za a ɗauka da kuma horas da su yadda ya kamata.

Ta ƙara da cewa shirin zai taimaka wajen shirye-shiryen ɗaukar jami’an ’yan sanda 50,000 tare da inganta kayayyakin more rayuwa da ake amfani da su wajen horas da jami’an tsaro.

Kara karanta wannan

Ana shirin 2027, Tinubu zai raba tallafin Naira biliyan 45

Bankin Duniya za ta tallafawa Najeriya
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Source: Getty Images

Ayyukan Bankin Duniya na dala biliyan 850

A taron, majalisar ta kuma amince da wasu manyan ayyukan raya ƙasa guda biyu da ake sa ran Bankin Duniya zai tallafa wa da jimillar dala miliyan 850.

Ayyukan sun haɗa da shirin Accelerating Resilience through Investment Systems and Engagement (ARISE-Nigeria), wanda zai ci dala miliyan 350, da kuma shirin bunƙasa yara ƙanana da zai samu dala miliyan 500.

Shirin ARISE-Nigeria na tsawon shekaru shida ne, kuma an tsara shi domin ƙarfafa ƙarfin Najeriya wajen shiryawa da tunkarar ambaliyar ruwa, fari, gobara da sauran bala'o'in yanayi.

Sanarwar ta bayyana cewa shirin zai inganta cibiyoyin ayyukan gaggawa, tsarin bayar da gargadi tun da wuri, sa ido kan yanayi da kuma hanyoyin samar da kuɗaɗen tunkarar bala'o'i a matakin tarayya da jihohi.

Ana sa ran jihohi biyar zuwa 10 za su shiga matakin farko na shirin, bisa la'akari da haɗarin bala'o'i, ƙarfin hukumominsu da kuma shirye-shiryen tunkarar matsalolin gaggawa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi alkawarin gyare-gyare da inganta jin daɗin aikin ’yan sanda

Buhari ya fi Obi farin jini - Shettima

An ji cewa mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya yi iƙirarin cewa Peter Obi ba shi da farin jinin da marigayi Muhammadu Buhari ya samu a Najeriya.

Shettima ya yi wannan furuci ne a Anambra yayin gangamin APC na neman wa’adin mulki na biyu ga Shugaba Bola Tinubu, tare da Gwamna Chukwuma Soludo.

Ya bukaci al’ummar Kudu maso Gabas su ƙarfafa alaƙa da sauran yankunan Najeriya, yana mai cewa samun goyon baya daga sassa daban-daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.