Muhammad Malumfashi
20016 articles published since 15 Yun 2016
20016 articles published since 15 Yun 2016
Za a ji cewa jam’iyyar NNPP ta samu karin kujerar majalisar dokoki a jihar Nasarawa. an samu wadanda su ka lashe zabe a APC, PDP, NNPP har da SDP a Nasarawa.
Man fetur yana cigaba da kara tsada a lokacin da rayuwa ta ke kara kunci. Har zuwa yanzu akwai fetur a Abuja, masu motoci suna shan lita ne a kan N675/l.
A yau ake jin Hukumar EFCC tayi nasara, kotu ta yankewa Mama Boko Haram da wasu hukuncin dauri. A. I Arogha shi ne lauyan da ya tsayawa EFCC a shari’ar.
Gwamnonin PDP sun ce Najeriya za ta bi tafarkin kasar Venezuela ko Bola Tinubu ya tashi tsaye. Gwamnonin PDP sun ce a nemawa al’umma mafitar kangin tattalin arziki.
Rahoton AuGF ya fallasa yadda ake bushasha da dukiyar gwamnati a ma’aikatu. Wasu ma'aikatu sun saba kashe fiye da abin da aka yi masu tanadi a kasafin kudi.
A shari'ar hukumar EFCC da Godwin Emefiele aka gano Muhammadu Buhari da Boss Mustapha sun amince a fitar da N2.9bn saboda aikin zaben 2023, yanzu ana kotu.
Adams Oshiomhole ya ce mutane na cin kwa-kwa daga manufofin APC. Sanatan Arewacin jihar Edo a majalisar dattawa ya fadawa ‘yan Najeriya cewa nan gaba za a more.
Za a ji kudin kasashen waje da aka adana a bankin CBN sun bace. Kuma ba za a iya cewa ga inda CBN ya boye kudin da EFCC ta karbo daga hannun barayi ba.
Za a samu labarin yadda Hukumar NDLEA mai yaki da safara da harkar miyagun kwayoyi ta damke wani Ahmed Mohammed da wasu mutane dauke da tulin kwayoyi.
Muhammad Malumfashi
Samu kari