Jami'ai Sun Kai wa Trump da Matarsa Dauki bayan Ɗan Bindiga Ya Kai Hari Taron White House

Jami'ai Sun Kai wa Trump da Matarsa Dauki bayan Ɗan Bindiga Ya Kai Hari Taron White House

  • An yi yunƙurin kai harin bindiga a wurin liyafar masu daukar rahoto daga fadar White House a birnin Washington, D.C. da ke ƙasar Amurka
  • Jami'an tsaro sun yi gaggawar kwashe shugaban Donald Trump da manyan shugabanni cikin gaggawa domin su tsira da rayuwarsu
  • Jami’an tsaro sun cafke wanda ake zargi, ana zarginsa da aikata laifin kai hari ga jami’in gwamnati da sauran tuhume-tuhume

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Washington DC, USA – Wani mai karfin halin, Cole Tomas Allen ya kai hari da daren Asabar, 25 ga watan Afrilu, 2026 kan liyafar shekara-shekara ta ‘yan jarida da fadar White House da ke Amurka.

Wannan hari ya sa liyafar ta rikide zuwa tashin hankali bayan wani mutum dauke da bindiga ya yi yunƙurin kutsawa cikin wurin taron da ke da tsauraran matakan tsaro.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: An kama mai taimaka wa yan bindiga su samu kudi a Sakkwato, ya fara bayani

An kai wa taron Donald Trump hari
Cole Tomas Allen da ake zargin ya kai wa su Trump hari, Donald Trump Hoto: Find Richard Holliday /Donald J Trump
Source: Getty Images

Washington Post ta wallafa cewa taron ya gudana ne a otal din Washington Hilton, inda manyan jami’an gwamnati da daruruwan ‘yan jarida suka hallara.

An kai hari kan su Trump

BBC ta wallafa rahotanni sun ce komai ya fara ne cikin natsuwa kamar yadda aka saba, kafin karar harbe-harbe ta karade harabar wurin binciken tsaron shiga taron.

Nan take jami’an SSS suka yi saurin zuwa kan dandali, suka fitar da shugaban kasa Donald Trump, uwargidan sa da mataimakin shugaban kasa JD Vance zuwa wani wuri na daban.

A cikin dakin taron kuwa, mutane sun rikice, inda da dama suka buya karkashin tebura yayin da jami’an tsaro dauke da makamai suka mamaye wurin domin kare lafiyar mahalarta liyafar.

An kama wanda ya harin taron Trump

An gano wanda ake zargi mai suna Cole Tomas Allen mai shekaru 31 daga jihar California, wanda ake zargin yana dauke da bindiga da wasu makamai shi ne ya yi yunkurin kai harin.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Ƴan fashi sun shiga teku, sun sace jirgin ruwa maƙare da ɗanyen mai

Jami’an tsaro sun ce ya harbi wani jami’in tsaro daga kusa yayin artabu a kofar shiga, amma rigar kariya ta hana harsashin huda jikinsa.

Bayan haka, jami’an tsaro sun yi nasarar kama shi nan take, yayin da jami’an ‘yan sanda da jiragen sama masu saukar ungulu suka kewaye wurin domin tabbatar da tsaro da kuma binciken yiwuwar samun wasu abokan aikinsa.

An kama wanda ake zargi da kai wa su Trump hari
Cole Tomas Allen lokacin da jami'ai suka yi ran da shi bayan yunkurin kai hari a Amurka Hoto: Find Richard Holliday
Source: Facebook

Bayan faruwar lamarin, Trump ya yi jawabi daga fadar White House inda ya tabbatar da cewa babu wani shugaban siyasa ko dan jarida da ya ji rauni.

Ya yabawa jami’an tsaro bisa jarumtaka, yana mai cewa wanda ya kai harin ya yi aiki ne shi kadai, ba tare da alaka da rikicin da ke gudana tsakanin Isra'ila da Iran ba.

Trump ya soke ganawar Amurka da Iran

A baya, mun wallafa cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya dakatar da tafiyar wakilansa zuwa birnin Islamabad, lamarin da ya soke zaman tattaunawa da Iran.

Trump ya bayyana cewa ya dauki wannan matakin ne saboda yadda ake ta kwan-gaba kwan-baya kan shirya zagaye na biyu na zaman sulhu a kan yaƙin Gabas ta Tsakiya.

Bayanai sun nuna cewa Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya bar birnin Islamabad bayan ganawa da jami'an Pakistan yayin da ake ci gaba da tsagaita wuta a yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng