Abu Ya Girma: Martanin Netanyahu kan Harin da Aka Yi Yunkurin Kashe Trump, matarsa
- Shugabannin duniya sun nuna goyon baya ga Donald Trump bayan harin bindiga a liyafar manema labarai ta Fadar White House
- Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da wasu shugabanni sun bayyana firgici kan harin, suna yaba wa jami’an tsaro kan gaggawar dakile maharin
- Shugabannin kasashe kamar Indiya, Pakistan da Taiwan sun yi Allah wadai da tashin hankali a siyasa, suna addu’ar samun lafiya ga jami’in dan sanda da ya jikkata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tel Aviv, Israel - Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi martani bayan wani harin dan bindiga a fadar White House yayin liyafa.
Netanyahu ya bayyana firgici kan harin bindiga da aka kai a liyafar manema labarai ta Fadar White House.

Source: Getty Images
Abin da Netanyahu ya ce kan farmakin Trump
Netanyahu ya bayyana haka ne a cikin wani sako da ya rubuta a shafin X a yau Lahadi 26 ga watan Afrilun shekarar 2026.
Firayim ministan ya bayyana cewa shi da matarsa Sara Netanyahu sun kadu sosai da samun labarin abin da ya faru.
Ya ce:
“Mun yi farin cikin cewa Shugaban kasa da uwargidan sa suna cikin koshin lafiya."
Ministan harkokin waje na Isra’ila Gideon Sa’ar ya ce kasarsa na tsaye kafada da kafada da Amurka, yana mai Allah wadai da harin da aka kai.
Ya kara da cewa ya yaba wa jami’an tsaro na Amurka saboda daukar mataki cikin gaggawa wajen dakile maharin tare da kare rayukan mahalarta taron.
Shugaban Isra’ila Isaac Herzog ya ce ya ji dadi da sanin cewa Donald Trump, Melania Trump da mataimakin shugaban kasa JD Vance ba su samu rauni ba.
Ya kara da cewa suna addu’a domin tsaro da zaman lafiya a Amurka bayan wannan mummunan hari, tare da fatan samun sauki ga jami’in da ya jikkata.
Ya ce:
“Muna godiya cewa jami’in tsaro da aka harba a harin yana cikin koshin lafiya kuma yana kan hanyar murmurewa.
“Daga Kasa Mai Tsarki, muna addu’a domin tsaro da zaman lafiya na Amurka da shugabanninta bayan wannan mummunan hari.”

Source: Getty Images
Firayim ministan Indiya ya yi martani
Firaministan Indiya, Narendra Modi da na Pakistan Shehbaz Sharif sun nuna damuwa kan harin, suna cewa tashin hankali ba shi da wuri a tsarin dimokuradiyya.
Shugabannin kasashe irin su Dominican Republic da Taiwan sun yaba wa jami’an tsaro, tare da nuna goyon baya ga al’ummar Amurka da addu’ar samun lafiya ga wadanda suka jikkata.
An cafke wanda ya kai Trump hari
A wani labarin, an ji cewa an samu karin bayani game da wanda ya kai hari a Fadar White House yayin Donald Trump da matarsa ke halartar liyafa.
Mutumin mai suna Cole Allen daga California ya kai hari da bindiga a wurin liyafar ‘yan jarida a Washington, inda aka fitar da Trump cikin gaggawa.
Rahotanni sun ce Allen mai shekara 31 ya shiga otel ɗin Washington Hilton dauke da makamai, ya harba harsasai kusa da wurin binciken tsaro.
Asali: Legit.ng

