Bincike Ya Bude Yadda Dala Biliyan 4 Suka Yi Kafa Daga CBN Lokacin Emefiele da Buhari

Bincike Ya Bude Yadda Dala Biliyan 4 Suka Yi Kafa Daga CBN Lokacin Emefiele da Buhari

  • Akalla $4,502,122,652 ya ragu daga cikin asusun da ake ajiye kudin kasashen waje a shekarar 2019
  • Bincike ya nuna kudin da ke asusun a 2018 ya ragu daga $42.59bn zuwa $38.09bn a shekara
  • Shaakaa Chira ba zai iya cewa ga inda CBN ya boye kudin da EFCC ta karbo daga hannun barayi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Kusan ba za a iya yin bayanin yadda wasu fam Dala biliyan 4.5 suka bace daga asusun ajiyar kudin wajen Najeriya ba.

Rahoton binciken da aka yi a OAuGF ya nuna kudi sun ragu daga asusun tsakanin 2018 da 2019, Premium Times ta kawo rahoton.

CBN Emefiele
Godwin Emefiele da Muhammadu Buhari a CBN Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Kudin da ke asusun CBN ya ragu

Daga binciken aka gano daga $42,594,842,852.75 a 2018, abin da ke asusun ya ragu zuwa $38,092,720,200.72 a shekarar 2019.

Kara karanta wannan

Watanni da sauka, masani ya tona yadda Buhari ya jefa Tinubu a ramin tashin Dala

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar ta ce wannan yana nufin ba a san yadda aka yi da $4,502,122,652.03 a CBN ba. Wannan ya faru a lokacin Godwin Emefiele.

Babban mai binciken kudin gwamnati, Shaakaa Chira ya ce bankin CBN bai yi wani gamsasshen bayanin inda aka kai dalolin ba.

CBN ya gaza magance gantalin Naira

Rahoton Shaakaa Chira ya ce ana cikin hadari a kan yadda aka gagara tsaida tangal-tangal da farashin kudin ketare su ke yi a kasar.

Bisa doka, sashe na 25 na dokar CBN ta shekarar 2027 ta wajabtawa bankin adana kudi a wannan asusu domin kula da tatalin arziki.

Daga rahoton aka fahimci kusan $8bn aka rasa a asusun da CBN ke ajiye kudin waje. Dukiyar ta ragu daga $44.7bn zuwa $35.7bn a 2019.

Ina kudin da EFCC ta gano?

Kara karanta wannan

FAAC: Yadda Aka Rabawa Gwamnoni da Ministan Abuja Naira Tiriliyan 6.5 a shekara 1

Bayan nan, bankin CBN ya gaza yin cikakken bayanin yadda aka yi da dukiyar satar da EFCC ta karbo daga shekarar 2016 zuwa 2019.

A kudin kasashen waje kurum, EFCC tayi nasarar karbo $40,502,645.06. Doka ta wajabta a sa kudin a asusun tarayya watau CRF.

EFCC na neman Godwin Emefiele

Zuwa yanzu ana da labari ana faman binciken Godwin Emefiele wanda ya rike bankin CBN tun 2014 kafin a dakatar da shi a shekarar bara.

A makon jiya aka ji EFCC ta ƙara tono badaƙalar zunzurutun kuɗi a kan tsohon gwamnan CBN da mai dakinsa, yanzu haka ana nemansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel