‘Yan Najeriya Na Shan Wahala a Mulkin Nan Ne Saboda Danyen Aikin Buhari – Sanatan APC

‘Yan Najeriya Na Shan Wahala a Mulkin Nan Ne Saboda Danyen Aikin Buhari – Sanatan APC

  • Adams Oshiomhole ya ce babu laifin Gwamnatin Bola Tinubu a kangin rayuwar da aka burma a halin yanzu
  • Sanatan ya ce Muhammadu Buhari ya kawo tsare-tsaren da su ka jawo ake kuka bayan an canza gwamnati
  • Ko lokacin da Muhammadu Buhari yake ofis, Adams ya ce shi da wasu a APC sun soki manufofin da aka kawo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Duk wahalar da ake kukan ana sha a yau, Adams Oshiomhole yana ganin ba su da dangantaka da tsare-tsaren Bola Tinubu.

Adams Oshiomhole ya cire hannun gwamnatin Bola Tinubu daga kangi da tsadar rayuwa, ya ce duk laifin Muhammadu Buhari ne.

Tinubu
Bola Tinubu da Muhammadu Buhari Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Channels ta rahoto Sanatan Arewacin jihar Edo a majalisar dattawa yana nunawa ‘yan Najeriya illar canza kudi da bankin CBN ya yi.

Kara karanta wannan

Wani jigo a APC ya gargadi Gwamnati, bai so ayi wa ma’aikata karin albashi sosai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da Tinubu ya cire tallafin fetur kuma ya saki farashin Dala a kasuwa, Adams Oshiomhole yana ganin ba shi ya kashe zomon ba.

A hirar da aka yi da ‘dan siyasar a gidan talabijin a makon jiya ya fadi matsayarsa.

Adams Oshimhole ya soki mulkin Buhari?

Oshiomhole wanda ya taba rike shugabancin APC a Najeriya yake cewa kullum yana fara sa kishin kasa kafin la’akari da batun jam’iyya.

A cewar Oshimhole, sai’ilin da Muhammadu Buhari ya kawo munanan tsare-tsare, shi da wasu sun nesanta kan su daga shugaban kasar.

Oshimhole yana ganin Buhari ya hada Tinubu da aiki

“Na fahimci ba abin da shugaban kasar ya yi alkawari kenan ba. Na nesanta kai na daga manufofin nan kuma ina farin ciki ba ni kadai ba ne.”
“Akwai gwamnonin da su ka tafi kotun koli domin yakar wadannan manufofi. Tasirin wadannan manufofin ne mu ke girbewa a yanzu.”

Kara karanta wannan

Kperogi ya fadi abin da zai faru idan Tinubu ya gaza shawo kan tsadar rayuwa a Najeriya

- Adams Oshiomhole

Kishin kasa ko kare gwamnati?

The Cable ta ce tsohon gwamnan na jihar Edo ya yi kokarin nuna Najeriya ce a gabansa ba wani ‘dan siyasa, mai mulki ko jam’iyya ba.

Duk da Bola Tinubu yana cikin jam’iyyar APC, Sanatan ya ce shugaban Najeriyan na yau bai rike da wani mukami cikin gwamnatin Buhari.

Saboda haka, tsohon Gwamnan ya ce ba za a zargi Tinubu da laifin ayyukan Buhari ba.

Gwamnatin Tinubu da 'yan kwadago

Idan ba a shawo kan hauhawar farashi ba, an ji labari shugaban NLC ya ce za a kawo dogon buri wajen maganar karin albashin ma’aikata.

Joe Ajaero ya ce sai an yi la’akari da halin da al’umma ta ke ciki a yanzu kafin a yanke sabon tsarin albashi,watakila su bukaci N1m.

Asali: Legit.ng

Online view pixel