Sata a CBN: Gwamnati Ta Roki INTERPOL a Kama Mutum 3 da Suka yi Amfani da Sa Hannun Buhari

Sata a CBN: Gwamnati Ta Roki INTERPOL a Kama Mutum 3 da Suka yi Amfani da Sa Hannun Buhari

  • Gwamnatin Najeriya ta hada da INTERPOL wajen damko wadanda suka saci $6.23m daga asusun CBN
  • Jim Obazee ya roki ‘yan sandan duniya su cafke mutane ukun da ake zargi a duk kasar da aka gansu
  • Jami’an tsaro za su fara farautar Adamu Abubakar, Imam Abubakar da Odoh Ochene a fadin duniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Gwamnatin Najeriya ta nemi agajin ‘yan sandan Duniya na INTERPOL wajen yin ram da wadanda suka saci kudi daga CBN.

Wasu sun yi amfani da sa hannun Muhammadu Buhari, an dauki $6.23m daga asusun bankin CBN kamar yadda aka rahoto a baya.

INTERPOL:Emefiele
Za a hada da INTERPOL a binciken Godwin Emefiele Hoto; Getty Images
Asali: Getty Images

Binciken Emefiele ta je wajen Interpol

Premium Times ta ce jami’in da aka kawo domin ya yi bincike na musamman a bankin CBN, Jim Obazee ya kai maganar zuwa gaba.

Kara karanta wannan

Ma’aikacin CBN Ya Fadawa Kotu Yadda Emefiele Ya Cire $6.23m Lokacin Zaben 2023

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mista Jim Obazee yana so jami’an INTERPOL su taimaka wajen ganin an damke sauran mutane ukun da ake zargi da wannan laifi.

Tsohon shugaban na FRCN ya aika da wannan bukata bayan samun takarda daga wata babban kotun tarayya mai zama a garin Abuja.

Su wanene Interpol za su cafko?

Ofishin mai binciken ya ce wadanda ake nema a badakalar babban bankin su ne: Adamu Abubakar, Imam Abubakar da Odoh Ochene.

Jaridar ta ce dama can hukumar EFCC ta yi karar Odoh Ochene wanda yanzu ya tsere.

Ana tuhumar Ochene da tsohon gwamnan CBN watau Godwin Emefiele a wannan kotu bisa zargin satar kudi da sunan aikin zabe.

EFCC ta ce Godwin Emefiele ya hada-kai da wannan mutumi aka yi amfani da ofishin sakataren gwamnatin tarayya aka cire $6.2m.

Gwamnati ta aika wasika zuwa Interpol

Kara karanta wannan

APC ta shirya kama mutum 16 da zarar an 'rantsar' da Nasiru Gawuna a Kano

A wasikar da aka aikawa Interpol, Daily Trust ta ce ana so a sa ido a kan wadannan mutane uku ta yadda za a iya cafke su a ko ina.

Da zarar an damke su, gwamnatin Najeriya tana so a dawo da su gida domin ayi bincike.

Hakan yana zuwa ne bayan kotu ta ba Obazee damar damke wadannan mutane duk inda aka gan su, an amince da hakan tun Junairu.

An dauki kudi a CBN da sunan Buhari?

Boss Mustapha ya bada shaida kan Godwin Emefiele a shari'ar da ake yi da hukumar EFCC a kotun tarayya kamar yadda aka ji labari.

Tsohon SGF ɗin ya bayyana cewa ba da sa hannun Mai girma Muhammadu Buhari aka fitar da kudi, an yi amfani da sa hannunsa ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel