'Yan Bindiga Sun Farmaki Dalibai da tsakar Sare, Sun Tafka Barna a Jami'ar OOU
- Yan bindiga sun kutsa dakunan kwanan dalibai na Jami'ar OOU da tsakar dare, sun yi awon gaba da abubuwa masu muhimmanci
- Bayanai daga mazauna yankin sun bayyana cewa daliban makarantar sun shiga yanayin firgici yayin harin, wasu da dama sun samu raunuka
- Rundunar yan sandan jihar Ogun ta ce ta tura jami'anta zuwa yankin domin gudanar da bincike kan abin da ya faru a gidan kwanan dalibai
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ogun, Nigeria - Wasu 'yan bindiga da ake zargin ‘yan fashi da makami ne sun kai hari dakunan kwanan dalibai a Jami’ar Olabisi Onabanjo (OOU) da ke Ibogun a jihar Ogun.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun bude wuta daga shiga cikin gidan kwanan da tsakar daren jiya Juma'a, lamarin da ya jefa dalibai cikin firgici yayin da suka rika guduwa domin tsira.

Source: UGC
Mahara sun bude wuta a dakunan kwana
Rahotan jaridar The Nation ya ce harin ya fara ne da tsakar dare, ya kuma ci gaba har zuwa safiyar Asabar, inda sama da mutane 12 dauke da makamai suka shiga dakunan kwanan dalibai da dama.
An ce maharan sun rika harbe-harbe domin tsoratar da dalibai kafin su kwashe wayoyi, kwamfutoci da sauran kayayyaki masu daraja.
Yadda daliban OOU suka shiga firgici
Wani mai amfani da kafar sada zumunta, Michael Mabayomije, ya bayyana cewa maharan sun yi aiki na tsawon lokaci ba tare da jami'an tsaro sun kai dauki ba.
Ya ce dalibai da dama sun jikkata a harin, yayin da wasu kuma suka shiga matsanancin firgici saboda tashin hankalin da suka gani.
Jaridar Punch ta kuma rawaito cewa an ga jini a bango da bene na daya daga cikin gidajen kwanan dalibai da abin ya shafa.
Mazauna Ibogun sun bayyana lamarin a matsayin mai tayar da hankali, inda suka ce karar bindiga ta karade harabar jami’ar yayin da dalibai ke kokarin tserewa domin ceton rayuwarsu
Wasu daga cikin wadanda abin ya shafa sun samu raunuka yayin da suke kokarin gudu ko kuma tsayawa kare kansu.

Source: Facebook
Wane mataki yan sanda suka dauka?
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, Oluseyi Babaseyi, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tuni jami'ai suka kaddamar da bincike kan lamarin.
Ya ce an fara bincike kan harin, tare da tura jami’an tsaro ciki har da DPO na yankin Ibogun da kuma kwamandan da ke kula da yankin domin duba halin da ake ciki da kuma kwantar da hankalin dalibai da mazauna yankin.
Jami'ar Summit ta musanta kai mata hari
A wani labarin, kun ji cewa wasu rahotanni da ake yadawa a kafafen sada zumunta sun nuna cewa 'yan bindiga sun kai kazamin hari kan dalibai a Jami'ar Summit da ke Kwara.
Hukumomin jami'ar wacce ke a shiyyar Arewa ta Tsakiya a Najeriya, sun musanta wannan jita-jita da ake yadawa, suna mai cewa labarin kanzon kurege ne.
Jami'ar ta bukaci iyaye da sauran al'umma su kwantar da hankulansu domin Jami'ar na cikin kwanciyar hankali, ta gargadi masu yada jita- jitar harin.
Asali: Legit.ng

