Gwamnonin PDP Sun Aikawa Bola Tinubu Sako Kan Mugun Hadarin da Ake Fuskanta

Gwamnonin PDP Sun Aikawa Bola Tinubu Sako Kan Mugun Hadarin da Ake Fuskanta

  • Gwamnonin jam’iyyar PDP sun yi zama na musamman a gidan gwamnatin Oyo da ke birnin Abuja
  • Bala Mohammed ya yi wa ‘yan jarida bayanin manufar haduwarsu bayan an tashi daga taron
  • Shugaban kungiyar gwamnonin na PDP ya bada wasu shawarwari ga gwamnatin Bola Tinubu

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Gwamnonin da aka zaba a karkashin jam’iyyar PDP sun kira taron gaggawa, inda suka tattauna a game da sha’anin kasa.

A karshen wannan zama da aka yi ranar Litinin, Premium Times ta ce gwamnonin sun nuna wajibi ne Bola Tinubu ya tashi tsaye.

Gwamnonin PDP sun aikawa Bola Tinubu sako
Gwamnonin PDP sun yi kira ga Tinubu Hoto:@Dolusegun16
Asali: Twitter

Gwamnonin PDP sun ce Tinubu ya farka

Gwamnonin adawan sun bukaci shugaban kasa ya fito da dabaru da za ayi amfani da su domin magance matsalar tsadar rayuwa.

Kara karanta wannan

Gwamnoni sama da 6 sun sa labule kan muhimmin abu 1 da ya shafi ƴan Najeriya, bayanai sun fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban gwamnonin PDP na kasa kuma gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammed, ya yi wa manema labarai jawabi bayan taron.

Gwamna Bala Muhammed ya ce sun tattauna a kan abubuwan da suka shafi Najeriya - abin da ya jawo kusan kowa yana wayyo Allah.

Tattalin arziki: Najeriya za ta bi layin Venezuela?

A game da batun yunwa, tsadar rayuwa da hauhawan farashi, an rahoto Bala yana cewa Najeriya ta kama hanyar kasar Venezuela.

Bala ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta hada-kai da duk masu ruwa da tsaki a samu saukin kuncin halin da al’umma su ka shiga a yau.

Gwamnan Bauchi yake cewa sun goyi bayan cire tallafin fetur amma a halin yanzu karyewar Naira ya haifar da tsadar rayuwa sosai.

Tinubu da matsalar tsaro a Najeriya

Kara karanta wannan

‘Yan Najeriya na shan wahala a mulkin nan ne saboda danyen aikin Buhari – Sanatan APC

Gwamnonin na PDP sun bada shawarar a hada karfi da jihohi domin ganin yadda za a magance matsalolin tattalin arziki da rashin tsaro.

Daily Trust a rahoton ta, ta ce gwamnonin jam’iyyar hamayyar sun nuna goyon bayansu ga batun kirkiro ‘yan sanda a matakin jihohi.

Kungiyar ta ce sai an bi matakai domin ganin ba ayi amfani da ‘yan sandan a keta alfarma ba.

Dangote zai taimakawa Kano

Mai kudin Afrika watau Aliko Dangote ya sha alwashin bada gudumuwa a mahaifarsa ta Kano kamar yadda labari ya zo a baya.

Dangote zai gina asibitin masu cutar sikila kuma zai gina wasu bangarorin a asibitin Murtala bayan rokon Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel