Farashin Fetur Ya Kai N700 Duk da NNPC Yayi Alkawarin Kudin Mai ba Zai Tashi ba

Farashin Fetur Ya Kai N700 Duk da NNPC Yayi Alkawarin Kudin Mai ba Zai Tashi ba

  • Farashin man fetur ya tashi sannu a hankali a wasu garuruwa, akwai wuraren da lita ta zarce N700 a yau
  • Masu motoci da babura a Borno su na zargin an lalata litoci, sun ce ana saida masu litar fetur a N750
  • Alkawarin da Kamfanin NNPCL ya yi game da canza farashin man fetur yana neman tashi a banza

Abuja - Kamfanin mai na kasa watau NNPCL ya yi ta kokarin gamsar da jama’a cewa babu dalilin kara kudin man fetur a Najeriya.

Ana haka kwatsam sai ga labari daga Daily Trust cewa ‘yan kasuwa sun yi karin farashi a wasu jihohi da ke Arewacin kasar nan.

Man fetur
Man fetur ya kara tsada Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Fetur ya kara kudi a garuruwa

Sauyin farashin da aka samu ya taba Sokoto da Borno da ke karshen shiyyoyin Arewa maso gabas da Arewa maso yamma.

Kara karanta wannan

NLC: Ma’aikata Za Su Bukaci N1m a Matsayin Mafi Karancin Albashi a Kowane Wata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Binciken da aka gudanar a farkon makon nan ya nuna ana saida litar man fetur ne tsakanin N690 zuwa N700 a gidajen man Sokoto.

A manyan gidajen mai kamar AA Rano da Dan Marna ne masu abubuwan hawa su ke sayen kowane litar man fetur a kan N675.

Rahoton ya ce a manyan gidajen NNPCL, har yanzu litar fetur ba ta wuce N620 ba.

Fetur ya kai N720 a Maiduguri

Da aka zagaya birnin Maiduguri da ke jihar Borno, an fahimci akwai inda litar man fetur ta wuce N700, ana saida ta ne a kan N720.

Akasin abin da aka samu a Sokoto, gidajen man NNPC wadanda na gwamnati ne, sun shafe mako guda ba su iya saida man fetur ba.

Direbobin da ke neman mai da araha sun ce kullum su ka zo gidan man NNPC ba su samun fetur, su kan samu gidan man ne a rufe.

Kara karanta wannan

Gasar AFCON: An shiga karancin rigunan Super Eagles a Kano, 'yan kwasuwa sun kwashi ganima

Idan mutum yana neman fetur dolensa ya hakura ya saye lita a kan akalla N700 a Borno watanni bayan cire tallafin mai a kasar.

Ana shan fetur da tsada

Masu abubuwan hawa suna zargin cewa litocin gidajen man ‘yan kasuwa bai da kyau, kusan a N750 ake saida masu litar fetur.

A Kano kuwa farashin bai kai haka ba, akwai inda ake sayen fetur a N620, a wasu wuraren sai mutum ya tanadi N675 zuwa N690.

Farashin da ake sayen fetur a garin Abuja bai kai haka ba, akasarin farashin N670 ne. Dama can 'yan kasuwa sun hango yiwuwar haka.

Taron Gwamnonin PDP

Venezuela kasa ce mai arzikin man fetur, amma sai ga shi ana fama da tsadar rayuwa da rushewar tattali duk da albarkar kasa.

Muddin Bola Tinubu bai tashi tsaye ba, an ji labari Gwamnonin da ke mulki a PDP sun ce Najeriya za ta bi tafarkin kasar Venezuela.

Asali: Legit.ng

Online view pixel