'Yan Bindiga Sun Takura da Hare Hare, Mutane da Dama Sun Bar Gidajensu a Sokoto

'Yan Bindiga Sun Takura da Hare Hare, Mutane da Dama Sun Bar Gidajensu a Sokoto

  • 'Yan bindiga sun addabi mutanen karamar hukumar Wurno ta jihar Sokoto da hare-haren da ke jawo asarar rayuka da dukiyoyi
  • Shugaban karamar hukumar ya bayyana cewa mutanen kauyuka da dama ba sa iya gudanar da rayuwarsa a matsugunansu
  • Ya bayyana cewa akwai sama da mutane 100 wadanda ke tsare a hannun 'yan bindiga bayan sun yi garkuwa da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Sokoto - Mazauna ƙaramar hukumar Wurno da ke jihar Sakkwato suna ƙara kaurace wa gidajensu da daddare sakamakon ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga.

Shugaban ƙaramar hukumar Wurno, Alhaji Abba Isa Sadiq Achida, ya bayyana hakan yayin da yake kokawa kan matsalar rashin tsaro.

'Yan bindiga na kai hare-hare a Sokoto
Gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Aliyu Sokoto Hoto: Ahmad Aliyu Sokoto
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai, a birnin Sokoto.

Kara karanta wannan

Gwamna zulum ya fadi manyan dabaru 2 da ke ba ƴan ta'adda damar kai wa sojoji hari

'Yan bindiga sun takurawa mutane a Sokoto

Ya ce lamarin ya zama babban abin damuwa ga mazauna yankin, gwamnatin jiha da ta tarayya, da kuma hukumomin tsaro, inda ya lura cewa yanzu ana kai hare-haren kusan kullum a sassan ƙaramar hukumar.

Shugaban ya koka cewa an yi asarar rayuka da dukiya da dama sakamakon ayyukan 'yan bindiga a shekarun baya-bayan nan, ya kuma ƙara da cewa sama da mutane 100 ne ke tsare a hannun masu garkuwa da mutane a faɗin yankin.

Mutane na barin gidajensu

Ya ce dubban mutane yanzu suna tururuwa zuwa garin Achida kowane yamma don kwanan a can, sannan su koma ƙauyukansu da rana.

“Suna kwana a makarantun firamare da duk wani fili da suka samu. Za ku iya tunanin irin tashin hankali da damuwar da suke fuskanta kowace rana."

- Alhaji Abba Isa Sadiq Achida

Sadiq Achida ya kuma nuna damuwa kan ayyukan mutanen da ake zargin masu ba da bayanan sirri ne waɗanda ke taimaka wa maharan, amma ya lura cewa al’ummomi sun fara tallafa wa hukumomin tsaro da bayanai masu amfani tare da kafa ƙungiyoyin sa-kai.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi da 'yan bindiga suka kai sababbin hare-hare a Plateau aka rasa rayuka

Ya ce ’yan bindigan suna tare manyan hanyoyi da daddare, musamman a ranakun kasuwar Achida da Goronyo.

'Yan bindiga na kai hare-hare a Sokoto
Taswirar jihar Sokoto, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

An yi kira ga gwamnati

Yayin da yake yaba wa Gwamna Ahmed Aliyu kan ƙoƙarin inganta tsaro, shugaban ya yi kiran da a gaggauta daukar mataki, ciki har da kafa sansanin sojoji a Achida.

Haka kuma ya yi kira da a samar da ƙarin ofisoshin ’yan sanda a Achida, Kwargaba, Chacho da sauran al’ummomin da ke cikin haɗari, tare da jaddada buƙatar samar da isassun ma’aikata da kayan aiki.

A cewarsa, ƙaramar hukumar ta fara aikin gyaran ofishin ’yan sanda na Achida domin karfafa ayyukan samar da tsaro.

'Yan bindiga sun yi kisa a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai wani mummunan hari a karamar hukumar Rogo a jihar Kano.

'Yan bindigan sun kashe mutum daya tare da jikkata wasu da dama, wanda hakan ya sa aka kara tsaurara matakan tsaro a yankin.

Maharan sun kai harin ne kan babura, sanye da kayan jami'an tsaro, inda suka farmaki wani dan kungiyar tsaro ta sa-kai mai suna Alasan Yellow.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng