NNPP Ta Yadu Zuwa Wajen Kano, Jam’iyya Ta Samu ‘Dan Majalisa a Jihar Nasarawa

NNPP Ta Yadu Zuwa Wajen Kano, Jam’iyya Ta Samu ‘Dan Majalisa a Jihar Nasarawa

  • Jam’iyyar ta tabbatar da kujerar majalisarta a jihar Nasarawa bayan zaben cike gurbi da aka shirya
  • INEC ta sake ayyana Musa Ibrahim Abubakar a matsayin wanda ya lashe zaben majalisar dokoki a Doma
  • ‘Dan majalisar ya yi nasara a jam’iyyar NNPP wanda ake gani tasirinta ya tsaya ne kurum a jihar Kano

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Nasarawa - Shugaban majalisar dokokin jihar Nasarawa, Danladi Jatau ya rantsar da wasu karin abokan aiki a majalisa.

Hakan yana zuwa ne bayan zaben cike gurbi da aka shirya a farkon watan Fabrairu, Leadership ta kawo wannan labari.

Rabiu Kwankwaso da NNPP
Masoyan NNPP wajen kamfe Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Wadanda aka rantsar a sakamakon nasarar da suka samu sun hada da Mohammed Adamu Omadefu a karkashin APC.

Kara karanta wannan

Kano: Dan Majalisar Tarayya a NNPP ya gwangwaje 'yan jam'iyyarsa da abin alkairi, ya fadi dalili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NNPP ta rike kujerar Doma a Majalisa

Rt. Hon. Danladi Jatau ya kuma rantsar da Musa Ibrahim Abubakar mai shekara 47 a duniya duk a ranar Litinin dinnan.

Hon. Mohammed Adamu Omadefu zai wakilci mazabar Keana shi kuma Musa Ibrahim Abubakar zai wakilci Doma ta kudu.

Shi Musa Ibrahim Abubakar ya sake lashe zabensa ne a karkashin NNPP mai alamar kayan dadi da kotu ta ce a sake zabe.

Danladi Jatau ya taya ‘yan majalisar murnar dawowa kan kujerarsu, rahoton ya ce an kuma yi kira da suyi aikinsu da kyau.

Majalisa ta rantsar da 'dan APC, NNPP a Lafiya

"Da farko ina so in taya Hon Mohammed Adamu Omadefu na mazaar Keana da Hon Musa Ibrahim Abubakar na kudancin Doma murnar lashe zaben 3 ga Fabrairu.
Mun yi murna da ku ka rike kujerunku domin wakiltar mazabunku a majalisar nan."

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Kwankwaso ya yi martani kan matakin Tinubu na fitar da abinci, ya roki jama'a

- Danladi Jatau

Premium Times ta ce 'yan majalisar sun yi farin cikin dawowa kan mukamansu.

NNPP ta bada mamaki a Nasarawa

Jihar Nasarawa tana daga cikin jihohin da aka san da zaman NNPP a Najeriya bayan farfado jam’iyyar da aka yi a farkon 2023.

Tsayawa takarar Rabiu Musa Kwankwaso a NNPP mai alamar yan marmari ya ba ta farin jini musamman a wasu jihohin Arewa.

Baya ga Kano, NNPP tana da kujerun majalisun dokoki da tarayya a Bauchi da Jigawa.

Siyasar jihar Nasarawa ta dauki salo na dabam a zaben 2023, an samu wadanda su ka lashe zabe a APC, PDP, NNPP har da SDP.

Jam'iyyar NNPP a zaben 2023

Kwanaki Buba Galadima ya fadawa Legit suna zargin an yi murdiya a zaben 2023 domin an rage masu kuri'u a Nasarawa da Bauchi.

Injiniya Galadima ya ce an yi wa NNPP magudin kuri’u fiye da 100, 00 a Nasarawa.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Ta yiwu Tinubu ya rufe iyakar Najeriya kan karancin abinci, ya fadi sauran hanyoyi

A Bauchi kuwa, 'dan siyasar ya shaida mana bincikensu ya nuna an yi wa jam’iyyar NNPP cogen kuri’u kusan 160, 000 a wasu garuruwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel