Muhammad Malumfashi
20016 articles published since 15 Yun 2016
20016 articles published since 15 Yun 2016
Mai kudin Afrika ya sha alwashin bada gudumuwa a mahaifarsa ta Kano. Aliko Dangote ya ji kiran Abba Gida Gida, ya zo Kano ya bunkasa tattalin arziki
Itse Sagay yana sa ran gwamnatin Bola Tinubu za ta kawo gyara a Najeriya amma Mai ba Shugaba Buhari shawara ya bayyana kuskuren Shugaba Tinubu a ofis.
Watsar da tsarin tallafin fetur ya jawo yunwa da wahalar rayuwa. Ministocin kasafi da na aikin gona su ka yi wa Sanatoci bayanin nan a majalisar dattawa.
Kudirin lantarki ya zama doka bayan sa hannun Bola Ahmed Tinubu a yammacin Juma’a. Dokar ta haramta raba wutar lantarki tsakanin jihohi da kasa a Najeriya.
Jama’atu Nasrul Islam ta nuna damuwa kan matsalar hauhawan farashin kayayyakin abinci da ake fuskanta a Najeriya, tayi kira ga shugaba Bola Tinubu da masu mulki.
Nentawe Yilwatda ya fadi yadda ake ci da addini, a yaudari mutane lokacin zabe a Jihar Filato. Duk ‘dan siyasar da aka likawa tambarin ‘dan takaran musulmai ya fadi.
Akwai masu neman cusa sunan Hon. Femi Gbajabiamila a badakalar N3bn ta ofishin Dr. Betta Edu. Rt. Hon. Tajudeen Abbas ya yi kaca-kaca da masu wannan zargi.
Gwamnoni sun dauki matakai domin rage tsadar abinci a Najeriya. Mai girma gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya sa hannu a kan matsayar da abokansa suka dauka.
Bola Tinubu ya ce a fito da shinkafa, masara ton 102, 000, 000, a rabawa talakawa. Ministan labarai ya sanar da matsayar da aka cin ma bayan zaman su a Aso Villa.
Muhammad Malumfashi
Samu kari