Hadimin Tinubu da Ya Ajiye Aiki Ya Shiga Takarar Kujerar Majalisar Tarayya a Kano

Hadimin Tinubu da Ya Ajiye Aiki Ya Shiga Takarar Kujerar Majalisar Tarayya a Kano

  • Tsohon hadimin Shugaba Bola Tinubu, Nasir Bala Ja’oji, ya ayyana shiga takarar kujerar majalisar wakilai a mazaɓar Tarauni ta jihar Kano gabanin 2027
  • Ja’oji ya bayyana cewa gogewarsa ta aiki a fadar shugaban ƙasa ta ba shi damar fahimtar dabarun shugabanci na gari da zai yi amfani da su
  • Dubban magoya baya ne suka fito tattakin nuna goyon baya ga Nasir Ja'oji a birnin Kano, lamarin da ya nuna cewa za a fafata sosai a mazaɓar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kano – Siyasar jihar Kano ta ƙara ɗumama yayin da Nasir Bala Ja’oji ya fito takarar neman kujerar mazaɓar Tarauni a Majalisar Wakilai.

Ja’oji ya gudanar da gagarumin tattaki na nuna goyon baya wanda ya faro daga Gadar Lado har zuwa sakatariyar jam’iyyar da ke Farm Centre.

Kara karanta wannan

Sarauniyar Kasar Hausa ta ayyana shiga takarar kujerar sanata a jihar Zamfara

Nasir Bala Ja'oji, tsohon hadimin Tinubu ya ayyana shiga takarar kujerar majalisar wakilai a Kano.
Nasir Bala Ja'oji, tsohon hadimin Tinubu da ya ayyana shiga takarar kujerar majalisar wakilai a Kano. Hoto: Ja’oji Media
Source: Facebook

Kano: Nasir Ja'oji ya ayyana shiga takara

Jaridar Punch ta ruwaito cewa daruruwan matasa da mata sun nuna goyon bayansu ga wannan aniya ta Ja'oji kuma sun fita tattakin tare da shi.

A jawabin da ya yi ga dubban magoya baya, Nasir Ja’oji ya bayyana cewa wannan takara ba ta son zuciya ba ce, face ta kishin mazaɓarsa:

"Wannan buri nawa bai samo asali daga sha’awa ta kashin kai ba, face daga kwadayina na son yi wa al'ummata hidima, da jajircewa, da kuma ci gaba da tuntuɓar mutane da akidun jam’iyyarmu mai girma." — Nasir Bala Ja’oji

Ja'oji: Gogewa don aiki a Tarauni

Nasir Ja’oji ya jaddada cewa zamansa a matsayin babban mataimaki ga Shugaba Tinubu ya ba shi horo na musamman kan yadda ake gudanar da shugabanci na gari da kuma gina ƙasa.

Ya bayyana cewa a lokacin da yake kan muƙamin, ya ba da gudunmawa sosai wajen tsara shirye-shiryen da suka shafi haƙƙin ɗanƙasa da kuma horar da matasa a faɗin Najeriya.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari da EFCC ke tuhuma kan zambar N2.8bn zai fito takara a Katsina

A cewarsa, wannan gogewa za ta taimaka masa wajen yin dokoki da za su amfani mutanen Tarauni, kamar yadda jaridar Independent ta ruwaito.

"Gogewar da na samu a matsayin Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa ta ƙara faɗaɗa fahimta ta kan harkokin gwamnati, gina ƙasa, da kuma shugabanci mai haɗa kowa."

- Nasir Bala Ja'oji.

Nasir Ja'oji ya bayyana ayyukan da zai shimfida wa Tarauni idan ya je majalisa.
Nasir Bala Ja'oji yayin da yake ayyana takararsa a mazabar Tarauni, jihar Kano. Hoto: Ja'oji Media.
Source: Facebook

Hasashen 2027 kan takarar Ja'oji

Ja’oji, wanda aka sani da shirye-shiryen tallafawa mata da matasa a yankin Tarauni, ya bayyana cewa ya daɗe yana bayar da gudunmawa ga nasarar jam’iyyarsa a matakai daban-daban.

Masu sharhi kan harkokin siyasa a Kano na kallon Ja’oji a matsayin wani babban jigo da zai iya girgiza fagen takara a mazaɓar Tarauni, duba da yadda jama'a suka fito da yawansu domin nuna masa ƙauna.

Wannan sanarwa tana nuna farkon fafatawa mai zafi da ake sa ran gani a mazaɓar ta Tarauni yayin da babban zaɓen 2027 ke ƙaratowa.

Ja'oji ya yi murabus daga gwamnatin Tinubu

A wani labari, mun ruwaito cewa, Nasir Bala Ja'oji, babban mai tallafa wa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi murabus, yayin da ake tunkarar kakar zaben 2027.

Kara karanta wannan

2027: An fara tsoron sanatan APC zai raunana aikin Tinubu bayan gana wa da Atiku Abubakar

Yanzu haka magoya bayansa sun fara shirin gudanar da gangamin tarbar sa a jihar Kano domin ƙarfafa masa gwiwa kan burinsa na gaba.

Ana sa ran cewa Nasir Ja'oji zai ƙaddamar da gagarumin yaƙin neman zaɓe a hukumance, don neman kujerar dan majalisar tarayya na mazabar Tarauni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com