Hadimin Ganduje Yayi Tonon Asiri, Ya Nemi Abba Ya Dawo da Sanusi, a Tsige Sarakuna 5

Hadimin Ganduje Yayi Tonon Asiri, Ya Nemi Abba Ya Dawo da Sanusi, a Tsige Sarakuna 5

  • Garba Kore ya dawo da maganar masarautun da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta kirkiro a Kano
  • ‘Dan siyasar ya na cikin wadanda suka goyi bayan a dawo da Muhammadu Sanusi II a kan karagar mulki
  • A lokacin baya shi yana cikin wadanda suka yi maraba da kirkiro sarakuna a Rano, Bichi, Gaya da Karaye
  • Kore ya ce tun farko sun kawo sarakunan ne domin su ci zabe, amma aka ba Gandujiyya kunya a 2023

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Garba Kore wanda ya yi aiki da Abdullahi Umar Ganduje a lokacin yana ofis, ya yi magana a kan batun masarautun jihar Kano.

An yi hira da Alhaji Garba Kore a tashar rediyon Express inda ya kawo shawarar a maida masarautar kasar Kano yadda ta ke kafin 2019.

Kara karanta wannan

Hukumar Hisbah a Kano ta kama fitacciyar jarumar TikTok, Murja Kunya

Muhammadu Sanusi II
Ana so a dawo da Muhammadu Sanusi II da Ganduje ya cire Hoto: @KYusufAbba @Dawisu @MSII_dynasty
Asali: Twitter

Sanusi II: Garba Kore ya caccaki Ali Baba

Kore ya yi tir da yadda tun farko Mai girma Abdullahi Umar Ganduje ya rika daukar shawarar mutane kamar su Alhaji Ali Baba Fagge.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shi Kore yana ganin Ali Baba suna cikin wadanda suka cuci Ganduje da APC a Kano, don haka ya ce kyau ayi watsi da shawarwarinsu.

A wani bidiyo da yake yawo, an ji mai ba tsohon gwamnan shawarar yana bayanin yadda suka zuga har aka cire Muhammadu Sanusi II.

Sarakunan Kano ba su ceci APC a 2023 ba

A tattaunawarsa da gidan rediyon, Garba Kore ya ce da farko ya rika kare sarakunan da aka kirkiro, amma ba su tsinawa APC komai ba.

Duk da babu ruwan Sarakuna da siyasa, jagoran na APC ya ji haushin yadda NNPP ta tika APC da kasa a masarautu uku a zaben 2023.

Kara karanta wannan

‘Yan Najeriya na shan wahala a mulkin nan ne saboda danyen aikin Buhari – Sanatan APC

A hirar aka ji Kore yana cewa a Bichi ne kurum jam’iyyar APC ta doke NNPP, ya alakanta nasarar da ‘yan majalisar tarayya na yankin.

Ana tunanin Barau Jibril da Abba Kabir Bichi su ka hana Ganduje shan kunya a Bichi.

Maganar Garba Kore a kan Masarautun Kano

"Idan kuwa zan fada a ji, sai an tsige ku. Yadda Ganduje ya koma kasa bai da komai a Kano, Wallahi ku ma sai kun koma."
"Da mu ka dasa su su biyar din, su dawo da gwamnatin mana. Mun nada su ne domin mu kuma cin zabe (a shekarar 2023)"

- Garba Kore

Yadda Ganduje ya canza masarauta a Kano

‘Dan siyasar ya ce tun farko son rai aka yi amfani da shi wajen kirkiro sababbin sarakuna da cire Mai martaba Muhammadu Sanusi.

"Sarakunan nan son zuciya ne ya kawo su, an nada su ne saboda gilli. Idan Ali Baba ya bada shawara aka tsige Sarki, to ni ina goyon bayan a rushe su."

Kara karanta wannan

AFCON: Ana saura kwana 4 aurensa ya rasu, cewar iyalan marigayi Ayuba a Kwara, bayanai sun fito

"Idan Abba Gida Gida zai yarda da mu yanzu, to ya dawo da Sanusi Lamido Sanusi. Shi ne ya cikawa ‘Yan Kwankwasiyya buri."
"Ni ina kaunar wanda ya zabe ni, ‘Yan Kwankwasiyya sun ba Abba Gida Gida kuri’a, suna jira a dawo da Sanusi Lamido Sanusi."

- Garba Kore

APC ta shirya cafke mutane a Kano?

Ana da labari wata takarda ta nuna an shirya cafke wasu mutane da zarar Nasiru Yusuf Gawuna ya yi nasara a kotu, an rantsar da shi.

Jerin dauke yake da sunayen Sunusi Bature Dawakin Tofa, Salisu Yahaya Hotoro da wasu ‘yan NNPP, amma APC ta musanya wannan zargi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel