Ana Hasashen Ruwan Sama Zai Sauka a Kaduna, Kogi da Jihohin Arewa 11 Yau Lahadi
- Hukumar NiMet ta fitar da hasashen yanayi na ranar Lahadi, inda ta ce za a samu ruwan sama da kuma tsawa a sassa daban-daban na ƙasar
- Yayin da za a fuskanci yanayin zafi a Arewacin ƙasar, NiMet ta ce jihohin shiyyar 12 za su fuskanci ruwan sama mai matsakaicin karfi
- NiMet ta shawarci jama'a da su kiyaye yin gudu yayin da suke tuka ababen hawa lokacin da ake ruwa domin gujewa hadurra saboda santsi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
NAJERIYA – Hukumar NiMet ta sanar da cewa ranar Lahadi za ta kasance mai cike da sauye-sauyen yanayi a faɗin jihohin Najeriya.
NiMet ta ce za a samu tsawa tare da saukar ruwan sama a jihohi 10 na Arewacin Najeriya da kuma wasu jihohin Kudancin kasar.

Source: Original
Wannan na kunshe ne a cikin hasashen yanayin da hukumar ta fitar a shafinta na X a yammacin Asabar, 25 ga watan Afrilu, 2026.
Hasashen yanayi a Arewacin Najeriya
Hasashen NiMet ya nuna cewa za a samu bullar hasken rana a Arewacin ƙasar a safiyar Lahadi, kuma ranar za ta iya zuwa da zafi.
Sai dai, NiMet ta ce ana sa ran samun tsawa da ruwan sama a wasu sassa na kudancin jihar Adamawa da Taraba tun da safen.
"Yanayin zafi zai mamaye jihohin Arewa a safiyar Lahadi, amma daga baya za a iya samun iska mai ƙarfi da ruwan sama a Kaduna, Bauchi, Gombe, Adamawa da Taraba." — NiMet.
Ruwan sama a Arewa ta Tsakiya
Babban birnin tarayya da kuma jihohin Arewa ta Tsakiya, irin su Nasarawa da Plateau za su kasance cikin yanayin gajimare da safe, kafin a fara samun ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi a lokacin yamma.
NiMet ta ce za a samu ruwan sama a Abuja da jihohin Nasarawa, Plateau, Benue, Kwara da Kogi a yammacin yau Lahadi.
Hasashen yanayi a Kudancin Najeriya
A kudancin ƙasar kuwa, yanayin zai kasance mafi tsanani inda za a samu ruwan sama kusan a dukkan jihohin yankin, ciki har da Akwa Ibom, Rivers, Cross River.
A yammacin ranar kuwa, za a samu ruwan sama a Lagos, Ogun, Oyo, Osun, Ekiti, Ondo, Edo, Delta, Bayelsa, Rivers, Cross River, Akwa Ibom, Abia, Imo, Anambra, Enugu, Ebonyi.
Wannan ruwa na iya haifar da ambaliya a wasu wuraren da kuma rincabewar zirga-zirga.

Source: Facebook
An sha ruwa a Katsina
Da misalin karfe 5:00 na yamma ne hadari ya hadu sosai a Funtua, jihar Katsina, kuma ruwa ya fara sauka kamar da bakin kwarya.
An shafe awanni ana ruwa, har zuwa bayan Magriba, yayin da aka ci gaba da yin yayyafi har zuwa bayan sallar Isha'i.
Amina Lawal Mailafiya ta bayyana wa Legit Hausa cewa:
"Yau kam mun sha ruwa sosai. Har yanzu da nake maka magana ana yayyafi. Tun da aka shiga damina, yau ne Funtua ta samu ruwa mai yawa irin haka."
Malam Nura Lawal shi ma ya tabbatar da cewa an samu ruwan sama a Funtua, inda ya ce:
"Mu za mu iya cewa yau ne damina ta kankama, don yau ne aka samu ruwan da ya game gari, kuma ya yi karfi sosai don har sai da katangun wasu gidaje suka rufta."
Shawarwarin NiMet ga jama'a
Domin kauce wa hatsari, hukumar ta fitar da waɗannan shawarwari:
- Iska mai karfi: A tabbatar an killace abubuwan da iska kan iya guduwa da su kafin a fara ruwa.
- Direbobi: Masu ababen hawa su rage gudu sakamakon rashin ganin gabansu sosai da kuma santsin titi yayin da ake ruwa.
- Kariya daga tsawa: An buƙaci jama'a su nemi mafaka a gidaje ko gine-gine masu ƙarfi muddin aka fara tsawa.
- Kamfanonin jirage: NiMet ta yi kira ga kamfanonin jiragen sama da su riƙa neman rahoton yanayi na musamman kafin tashi domin tabbatar da tsaron fasinjoji.
Duba hasashen a nan kasa:
NiMet ta gargadi kamfanonin jirage
A wani labari, mun ruwaito cewa, Hukumar NiMet ta yi hasashen cewa za a samu hazo da kura a wasu sassan Kano da jihohi 10 a Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan
Arewa da Kudu za su amfana da Tinubu ya nemi izinin sake ciyo bashin Dala miliyan 516
NiMet ta gargadi kamfanonin sufurin jiragen sama da su yi taka tsan-tsan don gudun samun hatsari sakamakon hazo, wanda zai haddasa rashin gani.
Ta kuma gargadi mutane masu fama da lalurar asma da sauran larurori masu alaka da numfashi da su kula da kansu matuka a yanayin da ake ciki.
Asali: Legit.ng


