Kwankwaso, Peter Obi Sun Hada Kai kan Takara a 2027, Ana Zargin Sun Ware Atiku

Kwankwaso, Peter Obi Sun Hada Kai kan Takara a 2027, Ana Zargin Sun Ware Atiku

  • Tsofaffin gwamnoni a Najeriya, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso na kokarin kafa tikitin hadin gwiwa a karkashin ADC
  • Majiyoyi sun ce suna shirin ne tare da jan hankalin shugabannin Arewa su mara musu baya kafin zaben fidda gwani na 2027
  • Rahotanni sun nuna cewa sun gabatar da tsarin mulki na wa’adi guda domin shawo kan manyan masu ruwa da tsaki na Arewa su janye goyon bayansu ga Atiku Abubakar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsofaffn yan takarar shugaban kasa, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso, sun kara kaimi wajen kokarin kafa tikitin shugaban kasa na hadin gwiwa.

Majiyoyi suka ce ana shirin ne karkashin ADC gabanin zaben 2027 inda suka fara tuntubar shugabannin Arewa domin samun goyon baya ga wannan shiri.

Neman takarar Obi, Kwankwaso da Atiku a ADC ta fara sauya salo
Atiku Abubakar (hagu), Peter Obi (tsakiya) da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso (dama). Hoto: Atiku Abubakar, Peter Obi, Rabiu Musa Kwankwaso.
Source: Facebook

Kwankwaso, Obi sun fara neman tikiti tare

Kara karanta wannan

Cin bashi: Fadar shugaban kasa ta yi wa Sanusi II martani kan sukar Tinubu

Majiyoyi daga cikin jam’iyyar wanda Punch ta samu, sun bayyana cewa shugabannin biyu na kokarin gabatar da tsarin wa’adi guda.

Suna yin hakan ne domin jawo hankalin masu ruwa da tsaki na Arewa su mara musu baya tare da janye goyon baya daga Atiku Abubakar.

Wannan yunkuri na daga cikin dabarar da suke bi domin tabbatar da mulki ya dawo hannun Kudu a 2027.

Rahotanni sun nuna cewa bangaren Rabiu Kwankwaso ya kara kaimi a makonnin baya-bayan nan, inda suka rika ganawa da sarakuna da sauran manyan shugabanni a Arewa da ke adawa da wa’adi na biyu na shugaban kasa mai ci.

Ana kuma bukatar Arewa ta bai wa Kudu damar kammala shekaru takwas a mulki, cewar rahoton TheCable.

Atiku na daga cikin masu neman takara a ADC
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar. Hoto: @atiku.
Source: Facebook

Yaran Kwankwaso da Obi sun hada tafiya

An kuma ruwaito cewa magoya bayan ‘yan takarar biyu sun kafa wata kungiya mai suna 'Obi–Kwankwaso Movement' domin bunkasa wannan hadin gwiwa kafin zaben fidda gwani na jam’iyyar.

Duk da haka, Atiku Abubakar ya bayyana cewa zaben 2027 zai zama na karshe da zai nemi shugabancin kasa.

Kara karanta wannan

Arewa da Kudu za su amfana da Tinubu ya nemi izinin sake ciyo bashin Dala miliyan 516

A halin yanzu, ana fuskantar rikicin shugabanci a cikin ADC mai adawa, yayin da ake jiran hukuncin kotun koli.

Duk da haka, ‘yan takara na ci gaba da tuntuba da neman goyon bayan juna domin tabbatar da nasara a zaben fidda gwani.

Dan ADC ya yi magana kan lamarin

Wani dan jam’iyyar ADC ya bayyana cewa akwai matsin lamba a cikin gida ga Atiku Abubakar, amma ya nuna shakku kan yiwuwar a kayar da shi, yana mai cewa yana da karfi a tsarin jam’iyyar.

Aliyu Abubakar ya kara da cewa ana sa ran shugabannin jam’iyyar za su taka muhimmiyar rawa wajen samar da matsaya guda kafin zaben fidda gwani.

Tikitin Obi da Kwankwaso na kara karfi

Mun ba ku labarin cewa maganar hadakar Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso na kara daukar hankali yayin da APC ke ci gaba da karfafa iko.

Wasu na ganin hadakar za ta kawo sauyi a zaben 2027, yayin da wasu ‘yan siyasa ke cewa ba za ta zama barazana ga gwamnati ba.

Rahotanni sun nuna cewa ana tattaunawa a boye kan tikitin hadaka, amma har yanzu akwai sabani kan wanda zai yi jagoranci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.