IPAC Za Ta Sa Kafar Wando Daya da Gwamnatin Kano Bayan Gano Take Taken Abba

IPAC Za Ta Sa Kafar Wando Daya da Gwamnatin Kano Bayan Gano Take Taken Abba

  • Wa’adin shugabannin kananan hukumomi 44 da kansiloli fiye da 400 ya cika a jihar Kano
  • IPAC tana zargin Abba Kabir Yusuf zai nada kantomomi a maimakon a shirya sabon zabe
  • Idan aka kawo shugabannin rikon kwarya, majalisar tana barazanar kai gwamnati kotu

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Ganin wa’adin zababbun shugabannin kananan hukumomi 44 ya cika a jihar Kano, IPAC ta fara maganganu daga gefe.

A ranar Laraba, Daily Trust ta rahoto majalisar IPAC ta na cewa Abba Kabir Yusuf yana shirin nada kantomomi a jihar Kano.

Kano.
Gwamnan jihar Kano da tsohon shugaban karamar hukuma Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

IPAC tana so a shirya zabe a jihar Kano

Majalisar ta IPAC ba ta goyon bayan nadin kantomomin rikon kwarya a maimakon a shirya zabuka a kananan hukumomi 44.

Kara karanta wannan

NNPP ta yadu zuwa wajen Kano, Jam’iyya Ta Samu ‘Dan Majalisa a Jihar Nasarawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan har gwamnatin Mai girma Abba Kabir Yusuf ba ta canza shawara ba, IPAC ta nuna a shirye ta ke da ta kai kara a kotu.

Majalisar IPAC ta fadi shirin da Abba yake yi

Mai taimakawa IPAC a wajen harkokin shari’a, Salisu Umar ya tara manema labarai a ranar Talata, ya ce za a nada kantomomi.

Salisu Umar ya yi ikirari cewa Mai girma Abba Yusuf zai dauko wakilan da ya aika zuwa kananan hukumomin su karbe mulki.

Kwanaki gwamnatin Kano ta tura jami’ai uku zuwa kowace karamar hukuma da sunan za su yi aiki da shugabanni da aka zaba.

IPAC ta ce jam’iyyu 12 daga cikin 18 da ke da rajista a kasar suna goyon bayan ta a wannan barazana da take yi wa gwamnan Kano.

Za a nada Kantomomi a Kano?

Kara karanta wannan

Hukumar Hisbah a Kano ta kama fitacciyar jarumar TikTok, Murja Kunya

Har zuwa yanzu, Mai girma gwamnan Kano bai tabbatar da yadda za a bi wajen maye gurbin shugabannin da suka sauka ba.

Da aka nemi jin ta bakin Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fadawa ’yan jarida cewa za a nada shugabanni a duka kananan hukumomi.

Darekta Janar na harkokin yada labaran ya ce Kwamishinan shari’a zai yi bayanin yadda za a bi wajen maye guraben da aka bari.

Kano: NNPP tana sassaka APC

Kwanaki aka kawo maku labari Auwalu Lawan Aranposu ya fito a mutum, zai koma jam'iyyar NNPP mai kayan marmari daga APC.

Kafin nan kuma Abdullahi Garba Ramat ya yi murabus daga matsayinsa na shugaban karamar hukumar Ungogo da ke Kano

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng