NiMet: Ana Hasashen Ruwan Sama Zai Sauka a Abuja da Jihohin Arewa 5 Ranar Juma'a
- Hukumar NiMet ta sanar da cewa za a samu yanayin zafi da rana a Arewa, yayin da za a yi ruwan sama a mafi yawancin jihohin Kudu
- Ana sa ran samun guguwa da iska mai karfi kafin fara ruwan sama, wanda hakan na iya haddasa hadari a tituna da kuma gidaje
- Yayin da NiMet ta jero jihohin Arewa biyar da za su iya samun ruwan sama a ranar Juma'a, hukumar ta gargadi direbobin da ke tuki ana ruwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja – Hukumar hasashen yanayi ta kasa (NiMet) ta fitar da jadawalin yanayin da za a fuskanta a fadin kasar nan ranar Juma'a, 24 ga watan Afrilu, 2026.
NiMet ta bayyana cewa za a samu sauyin yanayi daga zafi zuwa ruwan sama a sassa daban-daban, yayin da wasu jihohin za su fuskanci zafi kawai.

Kara karanta wannan
Laraba: Rana za ta yi zafi sosai a Arewa, za a samu ruwan sama a Neja da jihohi 7

Source: Original
Hukumar ta fitar da hasashen yanayin na ranar Juma'a ne a cikin sanarwar da ta fitar a shafinta na X a daren Alhamis, 23 ga Afrilu, 2026.
Hasashen yanayi a jihohin Arewa
A Arewa maso Yamma da maso Gabas, NiMet ta ce za a wayi gari da yanayin rana mai zafi a mafi yawancin jihohin shiyyoyin biyu.
Sai dai akwai yiwuwar samun tsawa da walkiya a wasu sassa na jihar Adamawa tun da safe. Daga baya kuma za a iya samun matsakaicin ruwan sama a Adamawa da Taraba.
A Arewa maso tsakiyar Najeriya, za a samu haduwar hadari a sararin samaniya, amma rana za ta hudo, ta kuma shiga cikin giza gizai lokaci zuwa lokaci.
Idan yamma ta yi, ana sa ran samun ruwan sama da tsawa a babban birnin tarayya Abuja da jihohin Benue, Kogi, Kwara.
Hasashen yanayi a Kudancin Najeriya
Hasashen NiMet ya kuma nuna cewa za a samu saukar ruwan sama a mafi yawan jihohin da ke a shiyyar Kudancin Najeriya.
Sai dai, NiMet ta ce za a fara samun ruwan a Akwa Ibom da Cross River tun da safe. Amma idan yamma ta yi, ruwan zai sauka a jihohin Legas, Ogun, Edo da Delta.
Sauran jihohin da za su samu ruwan sama hade da tsawa sun hada da Bayelsa, Rivers, Abia, Imo, Anambra, Enugu da Ebonyi.
Ana fargabar cewa wannan mamakon ruwa da zai sauka zai iya haddasa ambaliya a sassa daban daban na Kudancin kasar.

Source: Facebook
NiMet ta bada muhimman shawarwari
Hukumar ta fitar da wasu shawarwari domin kare kai daga hatsari:
- Mutane su yi hattara domin za a iya samun iska mai karfi; an bukaci mutane su killace abubuwan da iska kan iya dauka.
- An bukaci direbobi su rage gudu yayin da ake ruwa domin hanya tana santsi kuma gani yana raguwa.
- Mutane su guji bi ta hanyoyin da ruwa ke taruwa ko ya saba yin ambaliya.
- Idan ana walkiya, an bukaci mutane su nemi wurin buya domin kauce wa saukar tsawa..
Duba hasashen yanayin a kasa:
An bada mafita kan ambaliya a Arewa
A wani labari, mun ruwaito cewa, dattawan Arewa sun bukaci gwamnatoci da mutanen da ke zaune a yankunan da ambaliya ke yawan faruwa da su dauki matakan kariya.
ACF ta nuna damuwa kan hasashen da NIHSA ta fitar, wacce ta ce akalla garuruwa 1,249 a kananan hukumomi 176 na jihohi 30 da Abuja na fuskantar barazanar ambaliya.
Dattawan Arewa sun kuma bukaci hukumomin agaji su tanadi abinci, magunguna, ruwa da sauran kayan bukatu don tallafawa wadanda za su iya fuskantar ambaliya.
Asali: Legit.ng

