EFCC: An Daure Mama Boko Haram a Kurkuku Na Shekaru 10 Saboda Zambar N40m

EFCC: An Daure Mama Boko Haram a Kurkuku Na Shekaru 10 Saboda Zambar N40m

  • Aisha Alkali Wakil, Tahiru Alhaji Saidu Daura da Prince Lawal Soyade sun rasa shari’arsu da hukumar EFCC
  • Ana zargin wadannan mutane da karbar kudi har N40m da nufin za a kawowa wani Bawan Allah kayan aiki
  • Har zuwa yanzu babu kayan aikin kuma ba a dawo da miliyoyin ba, a dalilin wannan kotu ta garkame su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Borno - Alkali Umaru Fadawu na babban kotun jihar Borno da ke garin Maiduguri ya samu Aisha Alkali Wakili da aikata laifi.

A ranar Litinin, 12 ga watan Fubrairu 2024, hukumar EFCC ta sanar da cewa tayi galaba a shari’ar da ake yi da ita a kotun.

Mama Boko Haram
Mama Boko Haram za ta tafi kurkuku Hoto: Getyy Images
Asali: Getty Images

Mama Boko Haram a gidan kaso

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Gwamnan Arewa ya sharewa iyalai 70,000 hawaye, ya raba kayan abinci na miliyan 225

Mai shari’a Umaru Fadawu ya yankewa wannan mata da aka fi sani da Mama Boko Haram hukuncin dauri na shekaru goma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mama Boko Haram da Tahiru Daura da Lawal Soyade za su yi shekaru 10 a tsare a gidan gyaran hali bayan samunsu da laifi.

Sanarwar da hukumar EFCC ta fitar ta bakin Mista Dele Oyewale ta ce an samu wadannan mutane uku da laifin aikata zamba.

Laifin da Mama Boko Haram ta aikata

Jawabin ya ce kafin yanzu EFCC ta shiyyar Maiduguri ta samu Aisha Wakili da mutanenta da karbar kudin Bukar Kachalla.

Punch ta ce an yaudari shugaban kamfanin Hamiza Global Resources Limited za a kawo masa kaya daga kasar waje amma shiru.

A sakamakon abin da ya faru da Kachalla aka daure wadanda ake kara tun a 2020.

Alkali ya ba EFCC gaskiya a kotu

Kara karanta wannan

Kano: Kotu ta yi hukunci a shari'ar da mawaki ya maka BBC Hausa a kotu, bayanai sun fito

Kafin a fara wannan shari’a a kotu, mutanen da ake kara a kotun sun yi ikirarin ba su aikata laifuffukan da aka jefa masu ba.

Umaru Fadawu ya samu wadanda ake kara da laifi saboda haka ya yanke masu dauri na tsawon shekaru goma a gidan gyaran hali.

Baya ga daurin, Daily Post ta ce mutanen nan za su hadu domin maidawa Bashir Muhammad kudinsa N40m da aka karba.

A. I Arogha shi ne lauyan da ya tsayawa EFCC a shari’ar kuma ya gabatar da hujjoji 17 da mutane hudu domin su bada shaida.

Shari'ar EFCC da Godwin Emefiele

Da aka koma kotu, an samu labari Ogau Onyeka Michael ya ce yana ofishinsa a CBN a 2023 sai ga takarda daga wani Darektansu.

Abin da takardar ta ce shi ne a cire $6.23m daga bankin a biya masu lura da zabe, hakan ya jefa Godwin Emefiele a matsala.

Asali: Legit.ng

Online view pixel