Yajin Aiki: An Tashi Taron NLC da Gwamnati Baram-Baram ba Tare da Nasarar Komai ba

Yajin Aiki: An Tashi Taron NLC da Gwamnati Baram-Baram ba Tare da Nasarar Komai ba

  • Gwamnatin tarayya ba ta iya shawo kan ‘yan kwadago a zaman farko da aka yi a jiya kan maganar yajin-aiki ba
  • Nkeiruka Onyejeocha ta gayyaci shugabannin kungiyoyin NLC da TUC domin ta hana su abin da suke niyya ba
  • Bayanai sun nuna ba a iya cin ma wata matsaya a karshen taron da aka yi na ranar Talata a birnin Abuja ba

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja – Bisa dukkan alamu zaman da aka yi tsakanin wakilan gwamnatin Najeriya da ma’aikata bai haifar da wanin yaro mai ido ba.

Gwamnatin tarayya ta zauna da kungiyoyin kwadago bayan jin su na barazanar yin yajin-aiki, Punch ta kawo labarin yadda ta kaya.

Yajin-aiki NLC
Minista tana son hana yajin-aikin NLC Hoto: @NTANewsNow
Asali: Twitter

Minista ta hadu da ma'aikata kan yajin-aiki

Kara karanta wannan

Tsadar Rayuwa: An bukaci Shugaba Tinubu ya gaggauta yin murabus, karin bayani ya bayyana

Karamar ministar kwadago ta kasa, Hon. Nkeiruka Onyejeocha ta gayyaci kungiyoyin kwadago da ‘yan kasuwa a tattauna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NTA ta ce Onyejeocha ta na kokarin ganin ta hana ma’aikata yin yajin-aikin da suka yi niyyar farawa daga ranar 23 ga watan Fabrairu.

Idan abubuwa ba su sake zani ba, ma’aikatan sun huro wuta cewa za su koyawa gwamnati hankali saboda sabawa alkawuranta.

Matsayar NLC bayan zama da Minista

Wani jami’in NLC ya ce ma’aikatar kwadago ba ta da hurumin daukar wani mataki, iyaka su zama tsani tsakaninsu da gwamnati.

George Akume a matsayinsa na sakataren gwamnatin tarayya ya roki NLC su nuna kishin kasa, su kara hakuri da kokarin da ake yi.

Ministan yada labarai da wayar da kan al’umma, Mohammed Idris Malagi ya shaida cewa suna lallashin kungiyoyin kwadagon kasar.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Gwamnan Arewa ya sharewa iyalai 70,000 hawaye, ya raba kayan abinci na miliyan 225

Alhaji Mohammed Malagi yana sa ran ma’aikatan za su hakura da maganar yin yajin-aiki.

Masu abinci za su tafi yajin-aiki

A gefe guda kuma kungiyar masu toye-toye da girki a Najeriya sun ce daga ranar 27 ga watan nan za su tafi yajin-aiki a fadin kasar.

Muddin gwamnati ba ta cika yarjejeniyar da aka yi tun 2020 ba, kungiyar ta sanar da shugaba Bola Tinubu za ta dakatar da yin aiki.

Gwamnati ta sabawa ma'aikata alkawari

An ji labari Joe Ajaero da Festus Usifo a madadin NLC da TUC sun ce gwamnatin Bola Tinubu ba ta cika yarjejeniyar da aka yi da ita ba.

Kafin janye yajin-aiki a Nuwamban bara, sai da aka sa hannu a wasu ka’idoji wanda ‘yan kwadago suka ce an yi watsi da dukkansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel