Taba Mutuncin Sarkin Musulmin Najeriya da Matawalle Ya Jefa 'Yar Majalisar Amurka a Matsala
- An taso 'yar Majalisar Amurka, Kimberly Daniels kan maganganun da ta yi game da Sarkin Musulmi da Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle
- Kungiyar 'yan Najeriya mazauna Amurka ta yi barazanar daukar matakin shari'a idan yar Majalisar ba ta janye kalamanta kuma ta ba da hakuri ba
- Kungiyar ta jaddada cewa zargin da aka yi wa Sarkin Musulmi ba tare da hujja ba cin mutunci ne ga miliyoyin ‘yan Najeriya da ke girmama shi
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
America - Kungiyar ‘yan Najeriya mazauna kasar Amurka (NDMG-USA) ta yi barazanar daukar matakin shari’a kan wata ‘yar majalisar dokokin Amurka, Kimberly Daniels.
Kungiyar ta yi barazanar maka yar Majalisar a gaban kotu ne bisa kalaman da ta yi kan Sarkin Musulmin Najeriya, Muhammad Sa'ad Abubakar III, da kuma Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle.

Source: Facebook
The Nation ta rahoto cewa Daniels, wadda ke wakiltar mazaba ta 14 a majalisar dokokin jihar Florida karkashin jam’iyyar Democrat, ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya sauke Matawalle daga mukaminsa.
Haka kuma ta yi zargin cewa Sarkin Musulmi na da hannu a matsalar tsaro da ta addabi Arewacin Najeriya.
Martanin kungiyar NDMG-USA
A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Cosmas Collins, ya fitar ranar Juma’a, ya bayyana kalaman a matsayin marasa tushe da kuma cin zarafi.
Ya ce kungiyar za ta dauki matakin shari’a a Amurka idan 'yar Majalisa ba ta fito ta janye kalaman tare da neman afuwa ba.
“Sarkin Musulmi alama ce ta hadin kai da mutunci, wanda kullum yake kokarin tabbatar da zaman lafiya da sulhu a kasa,” in ji Collins.
Kare martabar Sarkin Musulmi
Kungiyar ta jaddada cewa zargin da aka yi wa Sarkin Musulmi ba tare da hujja ba cin mutunci ne ga miliyoyin ‘yan Najeriya da ke girmama wannan kujera.
Ta kara da cewa irin wannan furuci na iya jefa kasar cikin matsala da kuma bata mata suna a idon duniya, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
NDMG-USA ta ce duk da cewa ana iya sukar shugabanni, amma dole ne a yi hakan bisa hujjoji masu karfi, ba tare da yada jita-jita ba.
NDMG-USA ta kare ministan Tinubu
Ta kuma yi watsi da zargin da Daniels ta yi na cewa Matawalle ya yi kokarin rinjayar rahotannin duniya kan tsaro kuma ya yi yunkurin ba da cin hanci, inda ta ce ba a tabbatar da hakan ba.
Kungiyar ta bukaci ‘yan majalisun kasashen waje su rika yin taka-tsantsan wajen furta kalamai kan al’amuran Najeriya.

Source: Twitter
Ta ce yana da muhimmanci idan mutum zai yi magana irin wannan, ya yi ta bisa gaskiya da fahimtar halin da kasa ke ciki.
A karshe, kungiyar ta jaddada kudirinta na kare martabar Najeriya a idon duniya tare da inganta tattaunawa mai inganci kan matsalolin tsaro da ake fuskanta a kasar.
Matawalle ya maida martani ga Daniels
A wani rahoton, an ji cewa karamin ministan tsaron ƙasa, Bello Matawalle, ya yi martani kan zargin da wata yar majalisa a Amurka, Kimberly Daniels ta yi masa.

Kara karanta wannan
Jam'iyyar ADC ta kara girma, ta samu kujera mai gwabi a Majalisar Dattawan Najeriya
A sanarwar da ofishin karamin ministan tsaron ya fitar, ya musanta zargin da yar Majalisar ta yi cewa Matawalle ya yi yunkurin ba da cin hanci a Amurka.
Sanarwar ta ƙara da cewa Bello Matawalle bai taɓa shiga harkar cin hanci ba, kuma ba zai taɓa amincewa da duk wani aiki na rashin gaskiya ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

