NDLEA Sun Cafke Mai Ciki, Budurwa da Mai Taimakon Boko Haram da Miyagun Kwayoyi

NDLEA Sun Cafke Mai Ciki, Budurwa da Mai Taimakon Boko Haram da Miyagun Kwayoyi

  • NDLEA mai yaki da safara da harkar miyagun kwayoyi a Najeriya tayi babban kamu a wasu garuruwa
  • Femi Babafemi ya sanar da cewa an cafke wanda yake kai kwayoyi ga ‘yan ta’addan Boko Haram a Borno
  • Jami’an Hukumar NDLEA sun karbe lodin tabar wiwi, tramadol da wasu miyagun kwayoyi a makon jiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abuja - Hukumar NDLEA mai yaki da safara da harkar miyagun kwayoyi ta damke wani Ahmed Mohammed dauke da tulin kwayoyi.

Hukumar ta ce ana zargin Ahmed Mohammed ya boye miyagun kwayoyi da nufin kai wa ‘yan Boko Haram a yankin Banki a jihar Borno.

NDLEA
NDLEA ta cafke masu harkar miyagun kwayoyi Hoto: @ndlea_nigeria
Asali: Twitter

Jawabin Kakakin NDLEA

Mai magana da yawun bakin hukumar, Femi Babafemi ya sanar a wani jawabi da ya fitar a shafin X, ya bayyana nasarorin da aka samu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Gasar AFCON: An shiga karancin rigunan Super Eagles a Kano, 'yan kwasuwa sun kwashi ganima

Mista Femi Babafemi ya ce Mohammed yana cikin mutane 24 da aka kama bisa zargin safara da dillacin kwayoyi a fadin jihohin kasar.

An kama kwayoyi a jihohi 8

Babafemi ya ce daga cikin kamen da suka yi a jihohi takwas, an yi ram da wata mata mai cikin wata shida da zargin harkar kwayoyi.

Zuwa yanzu hukumar NDLEA tayi nasarar karbe fiye da kilogram 7, 609 na kwayoyi a kokarin da ake yi na ganin magance matsalar.

A ranar Juma’ar da ta wuce aka cafke Ahmad Mohammed a wani shinge da aka yi a Bama, ana bincikawa aka same shi da kwayoyi.

NDLEA ta ce an samu kwayoyin Tramadol 200 a hannun wannan mai shekara 42, ana zargin zai kai wa ‘yan ta’addan Boko Haram.

Amarachi Akaolisa mai shekaru 25 ita ce wanda aka samu da ciki, haka kuma an cafke wata budurwa Ifeoma Iheanyi a Anambra.

Kara karanta wannan

Kano: Kujerun Hajji 2,600 ne kacal aka sayar cikin 5,934

Wadannan mata su na cinikin Oraifite da Umuni-Evili a garin Aguleri da ke jihar Anambra.

NDLEA ta samu kwayoyi a Kano

Sauran wadanda aka cafke sun hada da; Okwuchukwu Chukwuka; Onyedika Ngwu; Ekene Hyginus da wani Nzomiwu Ikechukwu.

A hannunsu aka samu tabar wiwi, diazepam, codeine. Sannan an yi irin wannan kame a Nasarawa, Legas, Ondo da babban birnin Abuja.

A Kano an cafke wasu a Gadar Tamburawa, Bachirawa, Sabon Gari da sauran wurare da tramol. A ciki har da wani mutum mai shekara 58.

Sauran inda aka cafke mutane da kwayoyi sun kunshi jihohin Ogun, Edo da Yobe, don haka Babafemi ya yabawa aikin jami’an na su.

Sharrin 'yan bindiga

Ana da labari cewa miyagun 'yan bindiga na farautar Gwamnan jihar Katsina watau Dikko Umar Radda domin ganin bayan shi a duniya.

Bayanan sirrin harkokin tsaro sun nunawa Dikko Radda yana fuskantar barazana amma Gwamnan ya ce wannan bai dame shi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel