APC Ta Shirya Kama Mutum 16 Da Zarar An 'Rantsar' Da Nasiru Gawuna a Kano

APC Ta Shirya Kama Mutum 16 Da Zarar An 'Rantsar' Da Nasiru Gawuna a Kano

  • Jam’iyyar APC ta ce babu gaskiya a takardar da ake yawo da ita a kan niyyar cafke wasu Bayin Allah
  • Wata wasika da ake zargin ta fito daga sakatariyar APC ta bukaci ‘yan sanda su cafke mutane a Kano
  • Mafi yawan mutanen da aka samu sunayensu ‘yan adawar APC ne wadanda ke tare da gwamnatin NNPP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Ana yawo da takarda da ake ikirarin jam’iyyar APC ta rubutawa jami’an tsaro gabanin shari’ar zaben gwamnan Kano.

Wannan takarda da ake cewa ta fito a ranar 5 ga watan Junairu, tana dauke da tambarin sakatariyar APC ta reshen Kano.

APC-Nasiru Gawuna a Kano
Gawuna: Ana zargin APC da shirin cafke wasu Hoto: Salisu Yahaya Hotoro/Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

APC da jiran Gawuna Is Coming

A wasikar da aka aikawa ‘yan sanda, an nemi su cafke wasu mutane da zarar kotun koli ta tabbatar da Nasiru Gawuna a kan mulki.

Kara karanta wannan

NNPP ta yadu zuwa wajen Kano, Jam’iyya Ta Samu ‘Dan Majalisa a Jihar Nasarawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan takardar gaskiya ce, an zargi wadannan mutane da tunzura al’umma a kan gwamnatin APC, aka nuna za a maka su a kotu.

A karshe dai NNPP da Abba Kabir Yusuf ne suka yi nasara a shari'ar zaben 2023.

APC za ta 'cafke' mutane a Kano

Legit ta fara ganin takardar ne a shafin Malam Salisu Yahaya Hotoro wanda shi ne na farko a jerin wadanda ake da’awar za a damke.

Na biyu a jerin shi ne Aliyu Dahiru Aliyu, wanda ya ce bai san wani laifi da ya aikata ba.

...sunan 'Yan Kwankwasiyya

A jerin akwai fitattun ‘yan wasan kwaikwayo; Sani Musa Danja da Sanusi Oscar da ya fi shahara da Kwankwason Kannywood.

Akwai Sanusi Bature Dawakin Tofa wanda ya zama Darekta Janar na yada labarai a gwamnatin Mai girma Abba Kabir Yusuf.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta gama shiri, ta faɗi jiha 1 da zata ƙwace mulki daga hannun gwamnan PDP a 2024

Takardar tana dauke da sunan Hon. Auwalu Lawan Aranposu, wani tsohon shugaban karamar hukuma da ya koma NNPP.

Akwai Kabiru Sa'idu Dakata da Nasiru Zango sai kuma ‘yan siyasa irinsu Alhaji Alhajiji Nagodo da fitattun mata kamar A’i Jafaru.

Ina sunayen wadanda za a kama?

1. Salisu Yahaya Hotoro

2. Aliyu Dahiru Aliyu

3. Sani Musa Danja

4. Kabiru Sa'idu Dakata

5. Hon. Auwalu Lawan Aranposu

6. Sunusi Bature Dawakin Tofa

7. Sunusi Osca

8. Nasiru Zango

9. Kwankwason Dakata

10. Sufyan Safjamil Kabo

11. Ishak Abdul

12. Hajiya A'in Jafaru

13. Aminu Abdullahi Kima Darmanawa

14. Alhajiji Nagoda

15. Habu Tabule

16. Ibrahim Zakari Zawachiki

Sanarwa daga jam'iyyar APC

A wata sanarwa da mu ka samu daga shafin APC na reshen Kano, jam’iyyar ta karyata batun cewa an yi niyyar kama wasu mutane.

Jawabi da aka fitar a Facebook ta hannun Hon. Ibrahim Zakari Sarina ya ce babu kanshin gaskiya a batun tun daga adireshin ‘yan sanda.

Kara karanta wannan

Ma’aikacin CBN Ya Fadawa Kotu Yadda Emefiele Ya Cire $6.23m Lokacin Zaben 2023

Ibrahim Sarina ya ce suna fatan gaskiya za ta bayyana, asirin masu yada sharrin ya tonu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel