An Yi wa Gwamna Karan Tsaye bayan Nuna Magajinsa, Farfesa Ya Sha Alwashi

An Yi wa Gwamna Karan Tsaye bayan Nuna Magajinsa, Farfesa Ya Sha Alwashi

  • Farfesa Mohammed Sani Haruna ya bayyana matsayarsa kan takarar gwamnan Nasarawa bayan Gwamna ya nuna magajinsa
  • Farfesan ya ce ba zai janye takararsa ba duk da goyon bayan Gwamna Sule Abdullahi ga Sanata Ahmed Aliyu Wadada
  • Ya bayyana hakan ne bayan ganawa da masu ruwa da tsaki a Keffi, inda ya ce shawarar su ce za ta jagoranci matakin da zai dauka kan takararsa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Lafia, Nasarawa - Duk da cewa Gwamna Abdullahi Sule ya nuna goyon baya ga Sanata Ahmed Aliyu Wadada, an fara samun matsala.

Farfesa Mohammed Sani Haruna ya ce ba zai janye takararsa ba inda ya ce za a fafata da shi a zaben fitar da gwani.

An fara yi wa Gwamna Sule tutsu kan takara a Nasarawa
Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa. Hoto: Abdullahi Sule Mandate.
Source: Facebook

Haruna ya bayyana hakan ne a wani taron tuntuba da aka gudanar a Keffi tare da masu ruwa da tsaki da magoya baya daga yankuna uku na majalisar dattawa, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: An kama mai taimaka wa yan bindiga su samu kudi a Sakkwato, ya fara bayani

Mai neman takara a Nasarawa ya bijirewa gwamna

Tsohon mataimakin shugaban NASENI ya bayyana cewa zai shiga zaben fitar da gwani na APC a Nasarawa, yana mai jaddada cewa yana da hakkin tsayawa takara.

Ya ce manufar taron ita ce jin ra’ayin jama’a kan ko ya ci gaba da takara ko kuma ya janye domin samun matsaya guda.

Ya ce:

“Idan kun yanke shawarar cewa mu amince da hukuncin kuma mu janye daga wannan fafutuka, zan kada kuri’ar ‘eh’. Idan kuma shawarar wannan taro ita ce mu shiga zaben fidda gwani, wannan ba matsalata ba ce. Wannan shi ne ainihin dalilin wannan taro.
“Lokacin da gwamnati ta sanar da matsayarta, ‘yan takarar da ke cikin wannan dandalin sun amince cewa za mu tuntubi magoya bayanmu da muhimman masu ruwa da tsaki sannan mu dauki matsaya guda. Wannan ne ya sa ba ku ji wani bayani daga gare ni ba.”

Ya kara da cewa idan taron ya yanke shawarar janye takara zai amince, amma idan aka ce ya shiga zabe, hakan ba zai zama matsala gare shi ba.

Kara karanta wannan

Bayan boye boye saboda yaƙin Iran, Netanyahu ya fadi halin lafiyarsa

Wadada ya fara samun matsala a Nasarawa kan takara
Sanata Ahmed Aliyu Wadada da ake sa ran zai gaji Gwamna Abdullahi Sule a Nasarawa. Hoto: Ahmed Aliyu Wadada.
Source: Facebook

Farfesa ya ja layi kan takara a Nasarawa

Bayan tattaunawa mai zurfi, shugabannin jam’iyya daga yankuna uku sun amince cewa Haruna ya ci gaba da takara domin gwada farin jinin sa a zaben fitar da gwani.

Haruna ya ce wannan mataki ya biyo bayan bukatar hada kan magoya bayansa da suka dade suna tallafa masa a tafiyar siyasarsa, cewar Leadership.

Ya kuma bayyana cewa tun da farko sun amince da tuntubar magoya baya kafin daukar matsaya kan batun bayan sanarwar gwamnatin Abdullahi Sule.

Ya jaddada rawar da ya taka wajen kafa jam’iyyar APC, yana mai cewa ya bayar da gudummawar kudi da taimako wajen bude ofisoshi a kananan hukumomi.

Wasu daga cikin masu magana sun yabawa Haruna, suna mai cewa yana da farin jini a kasa da kuma gogewa da ya samu kafin shiga siyasa.

Gwamna Sule ya nuna wanda zai gaje shi

A wani labarin, an ji cewa Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ayyana Sanata Ahmed Wadada a matsayin wanda yake so ya gaje shi a babban zaɓen shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da maganar sulhu, Trump ya yi barazana mai ɗaga hankali ga Iran

Hukuncin gwamnan ya biyo bayan tattaunawa ta tsawon shekara guda da masu ruwa da tsaki da suka haɗa da sarakuna da kuma ƙungiyoyin matasa.

Gwamna Sule ya umarci dukkan masu riƙe da muƙaman siyasa a gwamnatin sa da su ajiye buƙatun kan su domin mara wa Sanata Aliyu Wadada baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.