Siyasar 2027: Fintiri da Gwamnonin Arewa 7 da Za Su Bar Mulki nan da Shekara 1
Siyasar Najeriya ta fara ɗaukar zafi yayin da gwamnoni bakwai masu faɗa a ji a shiyyar Arewa ke shirin barin gadon mulki gaba ɗaya a shekarar 2027.
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Wannan sauyi na shugabanci zai buɗe sabon babi na takara da kuma sauyin dabarun siyasa a jihohin da abin ya shafa, inda kowannensu ke ƙoƙarin barin tarihi mai kyau ta hanyar kammala manyan ayyukan da suka faro tun a shekarar 2019.

Source: Twitter
Gwamnonin Arewa da za su bar mulki
Rahoton cibiyar bincike ta ICIR ya nuna cewa, gwamnoni 10 ne za su kammala wa'adin su, amma bakwai ne ƴan Arewa.
Waɗannan gwamnonin sun gudanar da mulki a shiyyoyin Arewa Ta Tsakiya da Arewa Ta Gabas, inda suka mayar da hankali ga ayyukan raya ƙasa, tsaro, da lafiya.
Ga jerin gwamnonin Arewa da za su bar gadon mulki a 2027:
1. AbdulRahman AbdulRazaq (APC)

Source: Twitter
Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya hau mulki ne a matsayin gwamnan farko da ya karya daular siyasar Bukola Saraki da ta shafe shekaru tana mulkin Kwara, in ji rahoton Premium Times.
Gwamnatinsa ta ba da fifiko sosai wajen garambawul ga fannin ilimi da gyaran asibitoci domin zamanantar da jihar. Ana kallon nasarar sa a matsayin babban sauyi na tsarin shugabanci a jihar.
2. Abdullahi Sule (APC)
Abdullahi Sule, injiniya ne da ya yi amfani da gogewarsa ta ɓangaren kasuwanci wajen buɗe kofofin zuba jari da masana’antun jihar Nasarawa.

Source: Twitter
Kasafin kuɗinsa na 2026 na naira biliyan 545 ya mayar da hankali ne kan kammala ayyukan more rayuwa da aka riga aka fara, cewar rahoton Arise News.
Kodayake ya taɓa cewa ba zai ƙara neman muƙami ba, a watan Maris na 2026 ya sanar da cewa matasa sun matsa ya tsaya takarar Sanatan Nasarawa ta Arewa.
3. Ahmadu Fintiri (APC)

Source: Twitter
Ahmadu Fintiri ya girgiza siyasar jiharsa a farkon shekarar 2026 lokacin da ya sauya sheka daga PDP zuwa APC, matakin da ya sanya Adamawa zama reshen jam'iyya mafi girma a ƙasar.
Ya mayar da hankali ga gyaran makarantu da ƙarfafa matasa, kuma yanzu ana kallonsa a matsayin babban jigo a tafiyar Shugaba Bola Tinubu, in ji rahoton TVC.
4. Babagana Zulum (APC)

Source: Twitter
Babagana Zulum, farfesa ne da ya samu yabo a duniya wajen sake gina garuruwan da ta'addanci ya ruguza da kuma mayar da ƴan gudun hijira gidajensu.
Fannonin ilimi da tsaro ne suka tashi da kaso mai tsoka a kasafin 2026 na naira biliyan 890 da Zulum ya gabatar, cewar rahoton Business Day.
A gefe guda, jaridar Vanguard ta rahoto Babagana Zulum ya bayyana cewa ba shi da wani "ɗan lele" da zai gaje shi, inda ya ce ya bar wa Allah da jam'iyyar APC zaɓi.

Kara karanta wannan
Yadda sojoji da tsohon minista suka raba miliyoyin Naira don kifar da gwamnatin Tinubu
5. Bala Mohammed (PDP)

Source: Twitter
Sanata Bala Mohammed ya gudanar da mulkin sa ne wajen inganta asibitoci da ilimi yayin da yake fuskantar rikice-rikicen cikin gida na jam'iyyar PDP.
Bayan ganawarsa da Peter Obi, Legit Hausa ta ruwaito cewa Bala ya kwatanta kansa a matsayin "ɗan siyasa mai zaman kansa," wanda hakan ya bar tambaya kan inda makomar sa take a 2027 da bayanta.
6. Mai Mala Buni (APC)

Source: Facebook
Mai Mala Buni ya ba da ƙarfi wajen sake gina yankunan karkara da ta'addanci ya shafa, musamman makarantu da asibitoci, in ji rahoton Zagazola Makama.
Kasafinsa na shekarar 2026 na naira biliyan 515 ya mayar da hankali ga tallafa wa manoma da bunƙasa tattalin arziƙi. Yanzu haka tattaunawar wanda zai gaje shi tana ƙara zafi a sassan jihar Yobe.
7. Muhammadu Inuwa Yahaya (APC)

Source: Twitter
Jaridar Tribune ta rahoto cewa Gwamna Inuwa Yahaya ya samu karramawa daga ƙungiyar Sasakawa ta duniya sakamakon ayyukansa a fannin noma da kiwo.
Gwamna Yahaya ya kuma jagoranci ƙungiyar gwamnonin Arewa inda ya ba da fifiko kan tsaro. Ana ganin mulkinsa a matsayin wanda ya shimfiɗa harsashin ci gaba mai ɗorewa a jihar Gombe.
Jihohi 5 da zabensu zai dauki hankali
A wani labari, mun ruwaito cewa, gwamnonin da za su kammala wa'adi na farko sun fara shirye-shiryen neman tazarce domin yin zango biyu kamar yadda dokar Najeriya ta tanada.
Sai dai wasu gwamnonin na fuskantar kalubale mai girma a kokarinsu na neman wa'adi na biyu saboda bata wa da iyayen gidansu da kuma wasu malamai da suka shigo siyasa.
Kano na daya daga cikin wadannan jihohi biyar da za su fi daukar hankali sakamakon rabuwar Gwamna Abba Kabir Yusuf da uban gidansa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


