Gwamnonin Jihohin Arewa 10 da Za Su Nemi Tazarce a Zaben 2027

Gwamnonin Jihohin Arewa 10 da Za Su Nemi Tazarce a Zaben 2027

Akalla akwai gwamnoni 10 da ke Arewacin Najeriya da suke shirin sake neman tazarce a zaben shekarar 2027 da ake tunkara.

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Dukan gwamnonin sun samu nasara ne a zaben shekarar 2023 da Shugaba Bola Tinubu ya samu nasara.

Gwamnonin Arewa da za su nemi takara a 2027
Gwamna Abba Kabir, Dikko Umaru Radda da Gwamna Uba Sani na Kaduna. Hoto: Abba Kabir Yusuf, Dikko Umaru Radda, Uba Sani.
Source: Facebook

2027: Gwamnonin Arewa da ke neman tazarce

Rahoton Channels TV ya ce gwamnonin Arewa 10 ne suka samu nasara a zaben wanda ya zama wa'adinsu na farko a kan mulki.

Legit Hausa ta duba gwamnonin da aka zabe su a 2023 da ke neman wa'adi na biyu a Arewacin Najeriya.

1. Abba Kabir Yusuf - Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya samu nasara a zaben gwamnan jihar Kano a shekarar 2023 karkashin jam'iyyar NNPP.

Abba Kabir ya yi nasara ne da taimakon mai gidansa, Rabiu Musa Kwankwaso da ake ganin ya taka muhimmiyar rawa kan zaben.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya zubar da hawaye a taron nuna goyon baya ga Tinubu, an ji dalili

Sai dai daga bisani sun babe bayan Abba ya koma APC mai mulkin Najeriya yayin da Kwankwaso shi ma ya koma ADC, cewar rahoton Punch.

Kwankwaso da magoya bayansa na ganin Abba ya ci amanar tsohon gwamnan wanda wasu ke ganin zai fusakanci matsala a zaben 2027.

Abba ya babe da Kwankwaso bayan nasarar zaɓe a 2023
Sanata Rabi'u Kwankwaso da Abba Kabir Yusuf. Hoto: Rabi'u Musa Kwankwaso.
Source: Facebook

2. Uba Sani - Kaduna

Kamar Abba Kabir na Kano, Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya yi nasarar lashe zabe tare da goyon bayan Malam Nasir El-Rufai.

Uba Sani ya yi nasara ne karkashin APC wanda El-Rufai ya yi masa yaki domin ganin ya samu nasara a zaben.

Sai dai a yanzu, ba a tare domin an dade da babewa wanda ya kara rura wutar rikicin siyasa a Kaduna yayin da El-Rufai ya koma ADC daga baya.

Masana harkokin siyasa na ganin akwai jan aiki a gaban Uba Sani duba da tasirin El-Rufai duk da a yanzu yana kulle bayan tuhume-tuhume da ake yi masa.

Uba Sani ya raba gari da El-Rufai kafin zaben 2027
Gwamna Uba Sani na Kaduna da tsohon mai gidansa, Nasir El-Rufai. Hoto: Uba Sani, Nasir El-Rufai.
Source: Twitter

3. Dauda Lawal Dare - Zamfara

A yan kwanakin, Gwamna Dauda Lawal ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

Siyasar 2027: Fintiri da gwamnonin Arewa 7 da za su bar mulki nan da shekara 1

Kafin haka, Dauda Lawal ya sha takun saka da ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle da ake ganin zai zama masa barazana.

Dauda Lawal ya yi nasarar kwace mulki ne karkashin jam'iyyar PDP daga Matawalle wanda ke APC.

Sai dai ana ganin dawowar gwamnan zuwa APC ka iya rage masa fargaba kan zaben 2027 duk da yadda mutane suke sukar jam'iyyar.

Dauda Lawal ya dawo APC bayan takun saka da Matawalle
Gwamna Dauda Lawal Dare na jihar Zamfara. Hoto: Dauda Lawal.
Source: Facebook

4. Umar Namadi - Jigawa

Malam Umar Namadi na daga cikin gwamnonin Arewa 10 da iske shirin kammala wa'adinsu na farko a 2027.

Majiyoyi sun ce Gwamna Namadi da ke APC na samun matsala da tsohon gwamnan jihar, Mohammed Badaru Abubakar.

Hakan ne ma ya jawo ake ta yada jita-jitar cewa Badaru zai bar APC zuwa ADC saboda rikicin ya yi ƙamari.

Sai dai Badaru ya sha musanta hakan duk da cewa ana ganin rigimarsa da Namadi za ta iya yiwa gwamnan illa a 2027.

5. Dikko Umaru Radda - Katsina

Dikko Umaru Radda ya samu nasarar karɓar mulki daga hannun Aminu Bello Masari bayan nasarar da ya samu a 2023.

Kara karanta wannan

2027: An fara zargin Obi zai yaudari 'yan Arewa saboda ya muzguna masu a baya

Radda wanda dan APC ne na daga cikin gwamnonin da ake ganin ba su da wata kalubale a neman tazarce a siyasance.

Sai dai matsalar tsaro da ke damun jihar na daga cikin matsalolin da ka iya jawo matsala ga Radda a zaɓen.

Matsalar tsaro na iya jawo wa Radda cikas a Katsina
Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina a gidan gwamnati. Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda.
Source: Facebook

6. Ahmed Aliyu - Sokoto

Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto ya samu nasarar lashe zaben 2023 karkashin jam'iyyar APC.

Tun farkon hawan gwamnan, aka fara maganganu game da irin manyan kuɗaɗen da yake kashe kan wasu kwangiloli.

Hakan ya sa aka fara nuna shakku game da ayyukansa a jihar da ke fama da matsalar hare-haren ƴan bindiga.

Rashin tsaro a Sokoto da karfuin ADC na daga cikin barazanar da Ahmed Aliyu ke fuskanta game da neman tazarce da ya ke yi a jihar.

Gwamna Ahmed Aliyu na shan suka kan matsalolin tsaro
Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto yayin taro a gidan gwamnati. Hoto: @ahmadaliyuskt.
Source: Facebook

7. Agbu Kefas - Taraba

Gwamna Agbu Kefas ya samu nasarar darewa kan kujerar gwamnan Taraba bayan lashe zabe ƙarƙashin PDP.

Daga bisani, ya bi sahun sauran gwamnoni inda ya koma APC domin inganta rayuwar al'ummar jihar kamar yadda ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Dalilan da suka sanya Abba zabar Garo a mataimakin gwamnan Kano

An yi ta sukar gwamnan lokacin da ya koma APC duba da matsalolin da jihar ke fama da su na rashin ababan more rayuwa.

Tun 1999, kusan PDP ce kawai ke mulkin Taraba, wannan karo Agbu zai so ya canza tarihi.

8. Mohammed Umaru Bago - Niger

Gwamna Umar Bago na jihar Niger ya yi nasarar lashe zaben gwamna a karkashin jam'iyyar APC a 2023.

Gwamnan na fuskantar matsin lamba daga al'ummar jihar da dama game da rashin tsaro da ake fama da shi.

Wasu na ganin matsalolin tsaro na iya jawo masa cikas a zane da za a gudanar a shekarar 2027 domin neman tazarce.

Bago na daga cikin gwamnonin da ke neman wa'adi na 2
Gwamna Umaru Bago na jihar Niger. Hoto: Mohammed Umaru Bago.
Source: Twitter

9. Caleb Mutfwang - Plateau

Gwamna Caleb Mutfwang na daga cikin gwamnonin PDP da iska suka sauya sheka zuwa APC kafin zaben 2027.

Mutfwang ya sha da kyar a kotun zaɓe bayan kammala zaɓen 2023 wanda APC ke korafi kan halascin nasarar da ya samu.

Daga bisani, ya yi nasara a kotu kafin daga baya ya sulale zuwa jam'iyyar APC da ya ce ita ce mafita.

Kara karanta wannan

Kano da wasu jihohin Arewa 4 da zaben gwamna zai dauki hankali a 2027

10. Rabaran Hyacinth Alia - Benue

Bayan kammala karatun 'Diploma' a bangaren addinin Kirista da samun digiri a bangaren addini a 1990, fasto Hyacinth Alia ya zama babban Fasto.

An zabi Alia mai shekara 57 a zaben 2023 da ta gabata a karkashin tutar jam'iyyar APC a jihar da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya.

Gwamna Alia ya sha kai ruwa rana da sakataren gwamnatin tarayya, George Akume kan iko a APC wanda Bola Tinubu ya sha sasanta su domin ganin nasarar jam'iyyar.

Gwamna Alia na neman tazarce a Benue
Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benue. Hoto: Fr Hyacinth Alia.
Source: Twitter

Jihohin da zaben 2027 zai dauki hankula

A wani labarin, an ji cewa an fara shirye-shiryen zabukan 2027 a Najeriya wanda za a yi a farkon shekarar.

Yayin da zaben 2027 ke kara kusantowa, gwamnonin da za su kammala wa'adi na farko sun fara shirye-shiryen neman tazarce.

Har ila yau, akwai wasu jihohi musamman daga yankin Arewacin Najeriya da zabukansu zai fi daukar hankulan yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.