Yusuf Tuggar, Ministan Tinubu da Ya Yi Murabus Ya Ayyana Shiga Takarar Gwamna
- Tsohon Ministan Harkokin Waje, Yusuf Maitama Tuggar, ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan jihar Bauchi a zaɓen 2027 mai zuwa
- Tuggar, wanda tsohon ɗan majalisar wakilai ne, ya bayyana cewa bai fito neman takarar gwamna domin ya gina kansa ba, sai don gina al'umma
- Tsohon ministan ya lashi takobin ba wasu fannoni hudu muhimmanci da za su iya canja tarihin jihar Bauchi idan ya sami nasara a zaben na 2027
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Bauchi – Tsohon Ministan Harkokin Wajen Najeriya kuma tsohon ɗan majalisar wakilai, Yusuf Maitama Tuggar, ya bayyana aniyarsa ta neman kujerar gwamnan Bauchi a babban zaɓen 2027.
Tuggar ya yi wannan sanarwa ne a birnin Bauchi ranar Asabar, inda ya bayyana cewa lokaci ya yi da za a yi amfani da dimbin arzikin jihar domin amfanin talakawa maimakon son zuciya.

Kara karanta wannan
Ganduje ya yi karatun ta natsu, ya gano dalilin da ya sa ake yawan samun mabarata a Arewa

Source: Twitter
Yusuf Tuggar ya ayyana shiga takarar gwamna
Tuggar ya nuna damuwarsa kan yadda jihar Bauchi take da albarkatu masu yawa, amma har yanzu akwai talauci da rashin ingantaccen ilimi da asibitoci da suka addabi mazauna jihar, in ji rahoton Daily Trust.
Ya ƙara da cewa kwarewar da ya samu a ɓangaren kasuwanci da noma za ta taimaka masa wajen fuskantar ƙalubalen da manoma da masu kiwo ke fuskanta.
Tuggar ya bayyana noma da raya karkara a matsayin ginshiƙan shirinsa na gwamnati, idan har al'ummar Bauchi suka zabe shi a matsayin gwamnansu a 2027.
Ya lashi takobin cewa zai samar da ingantattun hanyoyi da wuraren adana amfanin gona domin sanya aikin noma ya zama mai riba ga talaka.
Dalilin tsohon minista na shiga takarar gwmna
Dangane da dalilin sa na tsayawa takara, Tuggar ya bayyana cewa:
"Wannan shawara tawa ta tsayawa takara ta samo asali ne daga muradina na inganta yanayin rayuwar mazauna jihar Bauchi da kuma buɗe hanyoyin samun arzikin jihar, ba wai don neman muƙami na kashin kai ba."
Kazalika, ya jaddada mahimmancin biyan albashin ma'aikata akan kari, inda ya ce hakan na ɗaya daga cikin manyan hanyoyin tabbatar da walwala.
A fannin tsaro kuwa, Tuggar ya ba da shawarar yin amfani da tsarin tsaro na al'umma da kuma tattaunawa, tare da haɗa kai da sarakunan gargajiya domin dawo da zaman lafiya.

Source: Original
Ilimi, kiwon lafiya, da matasa
Har ila yau, Tuggar ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta kafa wuraren koyar da fasaha na zamani (technology hubs) domin bai wa matasa damar samun ayyukan yi, in ji rahoton The Nation.
A fannin kiwon lafiya, ya yi alkawarin inganta asibitocin gwamnati da kuma ba da kulawa ta musamman ga lafiyar uwa da jinjiri.
Tuggar, wanda ya taba tsayawa takarar a shekarar 2011 da 2015, ya ce shekarun da ya shafe a ɓangaren adawa sun koya masa juriya da kuma sanin ainihin abin da talakan Bauchi yake buƙata.
Tuggar ya ajiye mukamin minista
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Ambasada Yusuf Tuggar, ya yi murabus daga mukaminsa na ministan harkokin waje a ranar 30 ga watan Maris, 2026.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Tuggar ya ajiye aiki ne domin ya nemi kujerar gwamnan Jihar Bauchi a babban zaɓe na 2027 mai zuwa.
Ministan, wanda mamba ne a jam'iyyar APC mai mulki, ya mika takardar murabus daga mulaminsa ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Legit.ng

