Aisha Musa
9376 articles published since 09 Agu 2016
9376 articles published since 09 Agu 2016
Hajiya Ramatu Tijjani, ta bawa talakawan zawarawa da marayu na addinin kirista 50 kautar kaji da abinci don suyi bukin Easter. Ramatu tace tayi hakan ne domin tallafawa talakawa don gina kyakkyawar alaka tsakanin mutane.
Rahotanni sun kawo cewa hukumar dake shirya albashin ma’aikata na gwamnatin tarayya da alkalai ta kasa wato RMAFC ta jaddada cewa alawus na naira miliyan 13.5 da sanatoci ke karba ya sabama tsarin tan a biyan ma’aikatan gwamnati.
Kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa Buhari ta kasa (BCO) ta yi kira ga yan siyasa da su daina buga kwalayen siyasa dauke da fuskar shugaban kasa Muhammadu Buhari a kwalayen yakin neman zabensu, cewa za'a yi musu kallo daya.
TY Danjuma ya bukaci ‘yan Najeriya dasu kare kansu daga ‘yan ta’adda, inda yace jami’an tsaro suna nuna son kai ta fannin ayyukan da suke gudanarwa na kare kasa. Kungiyar shari'a ta kalli hakan a matsayin Allah wadai.
Jami’ar Ibadan, ta shirya korar dalibai 328, wadanda ke aji daya a jami’ar, bisa “sakamakon kunyatarwa da suka samu a jarabawa”, ta shekarar 2016/2017, shugaban makarantar ya bayyana haka, yace jami’ar ta kamala sunayen daliban.
Shahararriyar jarumar nan da tayi fice a harkar shirya fina-finan Hausa Maryam Both tayi raddi ga masu amfani da sunanta a shafukan yanar gizo. Jarumar tayi Allah ya isa ga masu amfani da sunan nata suna bata mata suna.
Sanata Dino Melaye, yace ya gano shirin da hukumar ‘Yan Sanda ta kasa keyi da gwamnatin jihar Kogi don su kasheshi ta hanyar yi masa allura akan hanyar zuwa jihar ta Kogi. Shiyasa suka dage akan sai anyi masa shari’arsa a jihar.
Daya daga cikin manyan dattawan arewa Tanko Yakasai, yace maganganun da Theophilus Danjuma yake yi bai kamata ace suna fitowa daga bakin dattijo kamar shi ba, saboda hakan ba girman shi bane, kuma son tada husuma ne.
Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da majalisar shirin samar da yalwataccen abinci mai gina jiki, wadda shi da kansa zai shugabanta. Mambobin majalisar sun hada da gwamnonin jihohin Kebbi ,Taraba, Filato, Legas, Delta da Ebonyi
Aisha Musa
Samu kari