Nigerian news All categories All tags
Wata Musulma ta rabawa kiristoci kaji da kayan abinci a jihar Kaduna don tayasu murnar Easter

Wata Musulma ta rabawa kiristoci kaji da kayan abinci a jihar Kaduna don tayasu murnar Easter

- Hajiya Ramatu Tijjani, ta bawa talakawan zawarawa da marayu na addinin kirista 50 kautar kaji da abinci don suyi bukin Easter

- Ramatu tace tayi hakan ne domin tallafawa talakawa don gina kyakkyawar alaka tsakanin mutane duk da bambancin addini

- Tace kiristoci a fadin duniya a satin nan ne zasu kama azumin kwanaki 40

Hajiya Ramatu Tijjani, ta bawa talakawan zawarawa da marayu na addinin kirista 50 kautar kaji da abinci don suyi bukin Easter.

Ramatu tace tayi hakan ne domin tallafawa talakawa don gina kyakkyawar alaka tsakanin mutane duk da bambancin addini

Ramatu tace: “Kiristoci a fadin duniya a satin nan ne zasu kama azumin kwanaki 40. Saboda haka akwai bukatar a tallafawa zawarawan da kaji da kayan abinci don suyi bukin Easter cikin farin ciki da annashuwa, da kamar yadda sauran kiristoci keyi a fadin duniya”.

Tace wannan matsalar tattalin arziki dake fama da ita a wannan kasar, ya hana mutane jin dadin shagulgulansu na al’adu da addinai, ta kara da cewa shiyasa take tallafawa zawarawan da aka barwa marayu don suji dadi kamar kowa.

KU KARANTA KUMA: An bude duka hanyoyin jihar Legas duk da zuwan Shugaban kasa - Yan sanda

Shugaban Cocin, Fasto Yohanna Buru, yayiwa Hajiya Tijjani na taimakon da tayiwa masu karamin karfin. Ya bukaci ‘yan Najeriya dasuyi koyi da irin wannan halin kirki, ba wai dole sai wanda kuke addini daya ba.

Ya kuma yi kira ga malamai dasu kara kokari wurin koyawa mabiyansu hanyoyin na kirki da kuma yin koyi da litattafan addini don magance matsalolin al’umma da ‘yan ta’adda masu labewa da addini suna aikata miyagun ayyuka.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel