Allah ya isa ga masu amfani da sunana a shafukan yanar gizo suna bata mun suna - Maryam Booth

Allah ya isa ga masu amfani da sunana a shafukan yanar gizo suna bata mun suna - Maryam Booth

Shahararriyar jarumar nan da tayi fice a harkar shirya fina-finan Hausa Maryam Both tayi raddi ga masu amfani da sunanta a shafukan yanar gizo.

Jarumar tayi Allah ya isa ga masu amfani da sunan nata suna bata mata suna. Ta kuma ce ita ta san mutuncin dan Adam ballantana malaman addini domin a cewarta ita daga gidan tarbiya ta fito.

Har ila yau jarumar tayi Allah ya isa inda tace bazata taba yafewa ba har duniya ta nade.

Allah ya isa ga masu amfani da sunana a shafukan yanar gizo suna bata mun suna - Maryam Booth
Allah ya isa ga masu amfani da sunana a shafukan yanar gizo suna bata mun suna - Maryam Booth

Kamar yadda kuka sani a makon da ya gabata ne aka zargi jarumar da sukar shugaban kungiyar Hisbah Mallam Aminu Ibrahim Daurawa inda tace yayi rashin adalci da munafurci sakamakon kin magana da yayi akan auren yar gwamnan jihar Kano wato Fatima Ganduje.

KU KARANTA KUMA: Duk da maganar Buhari; Jam’iyyar APC ba za ta cire Oyegun daga kujerar sa ba

An wallafa wannan labari ne da sunan jarumar a shafin Facebook, inda labarin ya bazu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng