Kira ga daukar makamai: Danjuma bai yi magana kamar dattijo ba - Yakasai

Kira ga daukar makamai: Danjuma bai yi magana kamar dattijo ba - Yakasai

Daya daga cikin manyan dattawan arewa Tanko Yakasai, yace maganganun da Theophilus Danjuma yake yi bai kamata ace suna fitowa daga bakin dattijo kamar shi ba, saboda hakan ba girman shi bane, kuma son tada husuma ne.

A ranar Asabar dinnan ne T.Y Danjuma yayi wani furuci, inda yake zargin Sojojin Najeriya akan basa yin aikin su tsakani da Allah, kuma da hadin bakin su ake kai dukkanin hare-haren da ake yi a kasar nan.

Yayi sanarwar ne a lokacin da ya halarci wani taro da aka gabatar a jami'ar jihar Taraba, inda ya shawarci 'yan Najeriya da kada su dogara da sojoji domin baza su iya kare su ba ya bukaci kowanne dan Najeriya da ya fita ya kare kanshi a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

A bayanin sa, Yakasai ya bayyana maganar T.Y Danjuman a matsayin magana marar ma'ana, inda yace furucin nashi zai iya tada rikici a cikin al'umma, wanda hakan ba zai haifarwa da kowa da mai ido ba.

Kira ga daukar makamai: Danjuma bai yi magana kamar dattijo ba - Yakasai
Kira ga daukar makamai: Danjuma bai yi magana kamar dattijo ba - Yakasai

A rahoton da majiyarmu ta samo, Yakasai ya ce, Maganar da Danjuma yayi ba magana bace ta dattawa. Saboda dattawa an san su da tunani da hangen nesa, ba wai kokarin tada rikici a cikin al'umma ba.

Ya ce gidan soja har yanzu suna ganin girman shi duk da ya bar aikin sojan shekaru 40 da suka wuce, kuma suna saka shi a cikin dattawan sojojin kasar nan. Kamata yayi yaje ya samu manyan shugabannin sojojin yayi magana da su ba wai ya zo yana yada rikici a cikin jama'a ba.

KU KARANTA KUMA: Sauya fasalin zabe: Majalisan dattawa za ta sake gabatar da dokar

Ya ce Danjuma yayi wadancan furucin ne saboda shawarar daya bawa shugaba Muhammadu Buhari game da batun fadan makiyaya da manoma bai yi na'am da ita ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng