Kungiyar CAN Ta 'Karyata' Trump kan Batun Kisan Kiristoci a Najeriya

Kungiyar CAN Ta 'Karyata' Trump kan Batun Kisan Kiristoci a Najeriya

  • Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi ikirarin cewa hare-haren da dakarun sojojin kasarsa suka kawo Najeriya sun sanya an daina kashe
  • Kubgiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) a jihohin Arewa 19 da Abuja, ta fito ta yi martani ga shugaban kasar na Amurka ya yi
  • Shugaban kungiyar ya bayyana cewa Trump bai son bayanan da suka dace kan abubuwan da ke faruwa a zahiri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) da ke jihohin Arewa 19 da babban birnin tarayya Abuja, ta yi martani kan ikirarin Shugaba Donald Trump cewa ya kawo karshen kashe Kiristoci a Najeriya.

Kungiyar CAN a Arewa ta yi watsi da iƙirarin na Donald Trump cewa dakarun sojojin Amurka sun kawo ƙarshen kashe Kiristoci a Najeriya.

CAN ta karyata ikirarin Donald Trumo
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump a fadar White House Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

CAN ta bayyana hakan ne a hannun shugabanta, Joseph Hayab yayin wata tattaunawa da jaridar The Punch, ranar Asabar, 27 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

'Mun gama da su': Trump a fadi yadda ya kawo karshen kisan Kiristoci a Najeriya

Wane martani CAN ta yi wa Trump?

Joseph Hayab ya soki maganar Trump, inda ya na ce kan cewa 'yan Najeriya, ba Kiristoci kaɗai ba, har yanzu ana ci gaba da kashe su da kuma yin garkuwa da su a jihohi da dama.

Ya ce sai dai kawai waɗanda rashin tsaron ya shafa da kuma Kiristoci a Najeriya ne za su iya bayyana ko an samu wani ci gaba na a-zo-a-gani a yanayin tsaro, inda ya jaddada cewa kashe-kashe da garkuwa da mutane har yanzu suna faruwa a faɗin ƙasar.

Hayab ya bayyana bayanin na Trump a matsayin iƙirari na siyasa wanda ya dogara ga bayanan rudarwa daga masu bada shawara waɗanda ba su fahimci yanayin tsaro a Najeriya ba.

“Mutanen da suka dace su faɗi ko Trump ya yi nasara su ne Kiristocin Najeriya ko Kiristocin Arewa, ba Trump da kansa ba. Amma mai yuwuwa yana samun bayanansa ne daga majiyar da ba ta dace ba. Ina tsammanin wasu daga cikin iƙirarinsa na siyasa ba su da kyawun da za su iya warware abubuwa."

Kara karanta wannan

"Ban cire rai ba"; Sanusi II ya ba ECOWAS shawara kan kasashen Nijar Mali da Burkina Faso

“Ya kamata Trump ya bar waɗanda abun ya ritsa da su su yi waccan shaidar, ba shi ba. Waɗanda abun ya ritsa da su, su ne mutanen da suka dace su faɗi ko duk abun da ya yi ya haifar da wata nasara."

- Joseph Hayab

CAN ta ce ba a daina kisa ba a Najeriya

Yayin da yake amincewa da ayyukan soji na Amurka na kwanan nan waɗanda suka farmaki gungun 'yan ta'adda, shugaban na CAN ya ce daukin bai kawo ƙarshen hare-haren 'yan ta'adda kan 'yan Najeriya.

“Dabarar da Amurka da Trump ke amfani da ita ba ta da kyawun gaske saboda bayan dakarun Amurka sun kai hari a Sokoto a watan Disambar da ya gabata, sun tafi hutu mai tsawo. Sun sake zuwa kwanan nan kuma sun kashe wasu kwamandojin ISIS, amma har yanzu ana kashe mutane a nan kowace rana."

- Joseph Hayab

CAN ta yi wa Donald Trump martani
Shugaban kungiyar CAN a jihohin Arewa da Abuja, Joseph Hayab Hoto: John Joseph Hayab
Source: Facebook

An ba gwamnarin Trump shawara

Hayab ya buƙaci gwamnatocin Amurka da su mayar da hankali wajen samar da tallafi na zahiri maimakon yin abin da ya bayyana da iƙirari na siyasa.

“Ba mu san waɗanda ke ba shi shawara ko suke ba shi labaran da ba gaskiya ba ne. Idan suna son kawo ƙarshen kashe 'yan Najeriya da gaske, su daina farfaganda ko labaran kafafen yaɗa labarai su mayar da hankali ga zahirin gaskiya, saboda ba na jin waɗanda abin ya ritsa da su za su so irin wannan iƙirari."

Kara karanta wannan

'Kashi 80 na matsalolin tsaro da suka addabi Sakkwato na da alaka da miyagun kwayoyi'

- Joseph Hayab

Alkalan kotun ICC sun kai karar Trump

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu alƙalan kotun hukunta manyan laifuffuka ta kasa da kasa (ICC) sun shigar da kara kan Shugaba Donald Trump da gwamnatinsa.

Manyan alkalan guda uku sun shigar da Shugaba Trump kara ne kan takunkumin da aka saka musu a shekarar da ta gabata watau 2026.

Alkalan sun shigar da karar ne a wata kotun Amurka, iinda suka nuna cewa matakan sun kasance wadanda suka sabawa doka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng