Yaran Jagoran 'Yan Bindigan da Suka Sace Janar Sun Sake Sabon Ta'addanci a Katsina
- 'Yan bindiga dauke da makamai sun sake kai hari a wasu kauyukan jihar Katsina da ke yankin Arewa maso Yamma na Najeriya
- Majiyoyi sun bayyana cewa 'yan bindigan yaran jagoran 'yan bindigan da suka yi garkuwa ne da marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar
- 'Yan bindigan sun hallaka mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka yayin mummunan harin da suka kai a karamar hukumar Matazu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - 'Yan bindiga sun kashe mutane a wani harin ta'addanci da suka kai a garin Sayaya da ke Ƙaramar Hukumar Matazu ta jihar Katsina.
Mummunan harin 'yan bindigan suka kai a Alhamis, 25 ga watan Yunin 2026 ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane bakwai, har da mace guda.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce mazauna yankin sun bayyana lamarin a matsayin ɗaya daga cikin mafi muni da aka gani a cikin watannin baya-bayan nan.
'Yan bindiga sun yi ta'addanci a Katsina
Sun ce harin ya tarwatsa ɗan kwanciyar hankalin da mutane suka fara amfana da shi bayan tura jami'an tsaro yankin.
Majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun afkawa Sayaya ne a safiyar ranar Alhamis, 25 ga watan Yunin 2026 suna harbe-harbe ba kakkautawa tare da jefa babban tsoro yayin da mazauna garin suka tsere daga gidajensu domin neman kariya.
“Muna barci muka ji ƙarar harbe-harbe. Mutane suna ta kururuwa, yara suna kuka, kuma kowa yana gudu ta ɓangarori daban-daban. Kafin maharan su tafi, mutanenmu bakwai sun riga sun amsa kiran Ubangiji."
- Wata majiya
A cewar mazauna garin, waɗanda abun ya ritsa da su sun haɗa da manoma da 'yan kasuwa waɗanda ke fatan komawa ga rayuwar yau da kullum bayan makonni da aka samu ɗan kwanciyar hankali.
Yaran jagoran 'yan bindiga sun yi barna
Mutanen garin sun yi zargin cewa maharan suna ƙarƙashin jagorancin wani fitaccen jagoran 'yan bindiga ne da ake tsoro, Kachallah Fulani Muhammad, wanda daɗewa sunansa ke da alaƙa da munanan hare-hare da garkuwa da mutane a kauyukan Matazu da yankunan da ke maƙwabtaka da su.
“Wannan shi ne mutumin da ya daɗe yana addabar ƙauyukanmu tsawon shekaru. Shi ne wanda ya yi garkuwa da Manjo Janar Rabe Abubakar Batsari (Mai Ritaya) da matarsa. Duk lokacin da muka ji sunansa, mun san matsala ce ta zo.”
- Wata majiya

Source: Original
Sojoji sun janye kafin harin
Mazauna yankin sun alaƙanta sabon tashin hankalin da janyewar dakarun sojoji na rundunar ‘Operation Fansan Yamma’ da aka yi kwanan nan, inda suka yi zargin cewa maharan sun dawo kusan nan take bayan sojojin sun tafi.
“Lokacin da sojojin ke nan, muna iya barci da idanunmu a rufe,” in ji wani dattijon al'umma. “Amma suna tafiya, 'yan bindigan sun dawo da sabon fushi. Muna jin kamar an yi watsi da mu ne.”
- Wata majiya
Zargin kai 'yan bindiga aikin Hajji
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Katsina ta yi magana bayan an zarge ta da daukar nauyin wasu 'yan bindiga zuwa aikin Hajji.
Gwamnatin ta yi watsi da zargin cewa ta ɗauki nauyin aikin hajjin wasu 'yan bindiga, inda ta bayyana iƙirarin a matsayin na ƙarya wanda ba gaskiya a cikinsa.
Ta ƙalubalanci waɗanda ke da hannu a cikin zargin da su kawo sahihan hujjoji waɗanda za a iya tantancewa domin ƙarfafa iƙirarin nasu.
Asali: Legit.ng