Sakon shugaba Buhari game da bikin Easter

Sakon shugaba Buhari game da bikin Easter

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi gargadi ga ‘yan Najeriya dasu guji maganganu na kiyayya da rashawa da ta’addanci

- Shugaban kasar yayi kira ga mutanen kasa dasu yi amfani da wannan dama ta wannan lokaci, suyi koyi da abubuwan da Yesu Almasihu yayi garesu

- Shugaban yayi godiya ga Ubangiji daya nuna mana wannan lokaci da zamuyi murna, muyi shagali duk da ‘yan matsalolin da muke fuskanta a kasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi gargadi ga ‘yan Najeriya dasu guji maganganu na kiyayya da rashawa da ta’addanci, ya kara yin kira ga mutanen kasa dasu yi amfani da wannan dama ta wannan lokaci “muyi koyi da abubuwan da Yesu Almasihu yayi garesu”.

Shugaban yayi godiya ga Ubangiji daya nuna mana wannan lokaci da zamuyi murna, muyi shagali,kuma mu fifita jindadin ‘yan uwanmu akan namu, duk da ‘yan matsalolin da muke fuskanta a kasa, mu daina maganganun kiyayya da ta’addanci a wannan kasa tamu.

Sakon shugaba Buhari game da bikin Easter

Sakon shugaba Buhari game da bikin Easter

Yayi magana kuma akan kokarin da gwamnatinsa tayi cikin shekaru uku da tayi a kan mulki na wanda ya kawo, ragowar farashin kayan abinci; Cigabata fannin gyaran titian, da hanyar jirgin kasa, da kuma gine-gine na cigaba a kasa; wanda hakan yasa Najeriya ta zama wurin saka hannun jari ga ‘yan kasuwa na kasashe duniya.

KU KARANTA KUMA: Manyan jami’an tsaro na kasa sun gano kullin da akeyi na lalata zaben 2019 - Fadar shugaban kasa

“Muna godiya ga Ubangiji, bisa ga dawowar ‘yan matan makarantar Dapchi da suka samu kwanaki 30 a hannun ‘yan ta’adda, yanzu sun koma hannun iyayensu.

"Ina fatan har sauran ‘yan matan Chibok da suka rage ba’a sako ba, za’a sakosu don su komawa iyayensu cikin kwanciyar hankali. Ina fatan zaku cigaba da addu’a har Allah yasa su dawo lafiya."

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Hukumar wasannin Najeriya na reshen Jihar Filato watau YSFON tace abin da ya dace shi ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake fitowa takara a zabe mai zuwa na 2019 ganin irin ayyukan alherin da ya kawowa Najeriya a mulkin sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel