Cigaban da Buhari ya kawo a fannin noman shinkafa kadai ya isa yasa a sake zabarshi - Lai Mohammed

Cigaban da Buhari ya kawo a fannin noman shinkafa kadai ya isa yasa a sake zabarshi - Lai Mohammed

- Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa cigaban da shugaba Muhammadu Buhari ya kawo tun hawansa gwamnati ya fitar da mutane da dama daga talauci

- Tace Cigaban da Buhari ya kawo ta fannin noman shinkafa ya isa yasa a sake zabarsa idan har yayi shawarar tsayawa takara

- Ministan labarai, Lai Mohammed yace cigaban ya fara ne ta hanyar bayar da basussuka ga manyan ‘yan kasuwa wanda hakan yayi sanadiyyar ragowar shigowa da shinkafa cikin kasar da 60%

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa cigaban da shugaba Muhammadu Buhari ya kawo tun hawansa gwamnati ya fitar da miliyoyin mutane daga talauci, ya kara da cewa hakan kadai ma ya isa yasa a sake zabarsa idan har yayi shawarar tsayawa takara.

Ministan labarai, Lai Mohammed yace cigaban ya farane ta hanyar bayar da basussuka ga manyan ‘yan kasuwa wanda hakan yayi sanadiyyar ragowar shigowa da shinkafa cikin kasar da 60% wanda yasa mafi yawan shinkafar da akeci a Najeriya yanzu wadda aka noma a kasar ce.

Cigaban da Buhari ya kawo a fannin noman shinkafa kadai ya isa yasa a sake zabarshi - Lai Mohammed
Cigaban da Buhari ya kawo a fannin noman shinkafa kadai ya isa yasa a sake zabarshi - Lai Mohammed

“Munaso muyi amfani da wannan dama don kira ga ‘yan Najeriya dasuyi jinjina da wannan kokari da gwamnati keyi na taimakawa manoman shinkafa na kasar nan. Saboda shinkafar tana da Inganci, da lafiya, kuma bata jima akan ruwa ko dakin ajiya ba ana ta faman jigila da ita ba.

KU KARANTA KUMA: EFCC ta gayyaci Okonjo-Iweala don tayi bayani kan yadda aka cire $250m daga kudin Abacha

“Sakamakon haka muke kira da mutanen kasar nan dasu bamu goyon baya don cigaba da wannan aiki na fannin noman shinkafa a kasar nan, don a taimakawa mutanen kasar nan da ayyukan yi saboda suna bukatar shi”.

A halin da ake ciki, Shugaban hukumar kula da tattalin arziki na kasa mai rukon kwarya, Ibrahim Magu ya bayar da umurnin gayyatar Mrs Okonjo-Iweala don har ma an aika mata da takardar gayyata, bisa ga kudin da aka cire ba tare da wani izini ba a ranar 2, 9, 16, da 18 ga watan Maris, 2015.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng