Ainihin alawus da ya kamata 'yan majalisa su rika karba - Hukumar RMAFC
- Hukumar RMAFC ta fayyace ainahin alawus da ya kamata ace yan majalisa na karba a ko wani wata
- A cewar hukumar, naira miliyan daya da dubu dari ne alawus din ko wani dan majalisa
- Ta kuma jadadda cewa naira miliyan 13.5 da suke karba baya cikin tsarin albashin da ake biyan ma’aikatan gwamnati
Rahotanni sun kawo cewa hukumar dake shirya albashin ma’aikata na gwamnatin tarayya da alkalai ta kasa wato RMAFC ta jaddada cewa alawus na naira miliyan 13.5 da sanatoci ke karba ya sabama tsarin tan a biyan ma’aikatan gwamnati.
Mai magana da yawun hukumar, Malam Ibrahim Mohammed ya bayyana cewa dole hukumar ta wanke kanta akan wadannan kudade da yan majalisa ke karba bayan albashinsu na wata.
Ya kuma bayyana cewa hukumar ta amince da naira miliyan daya da dubu dari a matsayin alawus da kowane dan Majalisa zai rika karba a ko wace wata.
KU KARANTA KUMA: Oshiomole zai maye kujerar Odigie-Oyegun na ciyaman a APC
A halin da ake ciki, a baya Legit.ng ta rahoto cewa Wata babbar kotun Najeriya dake zamanta a Legas, ta ce korafin da kungiyar nan mai rajin yaki da cin hanci (SERAP) ta shigar gabanta dake kalubalantar tsofin gwamnoni dake aiki a matsayin ministoci da sanatoci bisa karbar albashi tudu biyu, yana kan tsarin doka.
Tun a watan Oktoban shekarar da ta gabata kungiyar SERAP ta maka tsofin gwamnonin a kotu domin neman ta dakatar da su daga karbar albashi tudu biyu; a matsayin tsofin gwamnoni da kuma wanda suke karba a matsayin Sanatoci kk Ministoci a yanzu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng