Dino Melaye ya zargi ‘Yan Sanda da shirya kashe shi

Dino Melaye ya zargi ‘Yan Sanda da shirya kashe shi

- Sanata Dino Melaye, yace ya gano shirin da hukumar ‘Yan Sanda ta kasa keyi da gwamnatin jihar Kogi donsu kasheshi

- Shiyasa suka dage akan sai anyi masa shari’arsa a cikin jihar ta Kogi, maimakon birnin tarayya, bisa ga laifin da ake zarginsa akai

- Yace hukumar ‘Yan Sandan ta zargeshi da daukar nauyin ‘yan ta’adda da makamai akan hanyar filin jirgi na birnin tarayya

Sanata Dino Melaye, yace ya gano shirin da hukumar ‘Yan Sanda ta kasa keyi da gwamnatin jihar Kogi don su kasheshi ta hanyar yi masa allura akan hanyar zuwa jihar ta Kogi.

Shiyasa suka dage akan sai anyi masa shari’arsa a cikin jihar ta Kogi, maimakon birnin tarayya, bisa ga laifin da ake zarginsa akai.

Dino Melaye ya zargi ‘Yan Sanda da shirya kasheshi
Dino Melaye ya zargi ‘Yan Sanda da shirya kasheshi

Hukumar ‘Yan Sanda ta fadawa jaridar Premium Times cewa, zargin bashi da asali.

Melaye ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da BBC Hausa a ranar litinin. Yace, “Ina da ma biya kuma na riga na san dabararsu.

"Jimoh mashood mai magana da yawun hukumar ‘Yan Sanda da kuma Yahaya Bello Gwamnan jihar ta Kogi sun hade mani kai”, cewarsa.

Yace hukumar ‘Yan Sandan ta zargeshi da daukar nauyin ‘yan ta’adda da makamai akan hanyar filin jirgi na birnin tarayya.

Yace, “Ina tsoron zuwa Lokoja, saboda anyi kokarin kasheni har so biyu, na kai kara ga ‘yan sanda na fada masu ina zargin Ciyaman na karamar hukumar, an samu makamai a gidansa amma daga baya jami’an sun juya mani baya.”

KU KARANTA KUMA: Annoba ta kashe mutane 8 a kano

Bayan wannan zargi da ake masa na bawa ‘yan ta’adda makamai, Melaye yana fuskantar dawowa jiha daga majalisar Dattijai. Bayan haka kuma hukumar zabe mai zaman kanta INEC, zata cigaba kokarin mayar dashi jiharsu da zarar ta samu amincewar kotun daukaka kara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng