Akwai Matsala: Har Yanzu ba a Bai Wa Hukumar INEC Kudin Shirya Babban Zaben 2027 ba
- Hukumar zaben Najeriya, INEC ta ce har yanzu ba ta karɓi kasafin kuɗin da ta gabatar domin shirya zaɓen 2027 daga gwamnatin tarayya ba
- Ta ce duk da haka shirye-shiryen zaɓen na ci gaba kamar yadda doka ta tanada, yayin da take dakon a tura mata Naira biliyan 873.78
- INEC ta kuma bayyana shirinta na gudanar da zaben gwaji domin tabbatar da ingancin tsarin fasahar da za a yi amfani da shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa har yanzu ba ta karɓi kasafin kuɗin da aka ware domin gudanar da babban zaɓen shekarar 2027 ba.
Sai dai hukumar ta tabbatar da cewa hakan bai hana ta ci gaba da shirye-shiryen gudanar da zaɓen cikin nasara ba.

Kara karanta wannan
Bayan hukuncin kotu, NDC ta bayyana makomar takarar Peter Obi da Kwankwaso a zaben 2027

Source: Facebook
INEC tana jiran kuɗin zaɓen 2027
The Nation ta ruwaito cewa kwamishinan INEC mai kula da ilimantar da masu zaɓe da yaɗa labarai, Malam Mohammed Haruna, ne ya bayyana hakan a wani taron tattaunawa da aka gudanar a Abuja.
Taron ya samu halartar jami'an INEC, jam'iyyun siyasa da ƙungiyoyin fararen hula, inda aka tattauna kan zaɓen gwamnan Ekiti da kuma shirye-shiryen babban zaɓen 2027.
Haruna ya ce INEC ta gabatar da buƙatar kuɗi na Naira biliyan 873.78 domin gudanar da zaɓen 2027, wanda ya haɗa da kuɗaɗen gudanar da zaɓe, fasaha da sauran manyan ayyuka.
Dokar zaɓe ta tanadi lokacin sakin kuɗi
A cewarsa, har yanzu ba a karya doka ba saboda Dokar Zaɓe ta 2026 ta tanadi cewa dole ne a saki kuɗaɗen zaɓe ga INEC aƙalla watanni shida kafin gudanar da babban zaɓe.
Ya bayyana cewa duk da rashin sakin kuɗin, hukumar ta fara shirye-shiryen sayen sababbin na'urorin tantance masu zaɓe (BVAS) da kuma maye gurbin waɗanda suka lalace, suka ɓace ko kuma ba a dawo da su ba bayan zaɓukan baya.

Kara karanta wannan
A wata 1 kacal, hukumar kwastam ta tara kudin shiga sama da Naira biliyan 100 a tashar TinCan
Haruna ya ce:
"Daraktan sashen ICT ya dawo daga ƙasar China bayan tattaunawa kan sayen sababbin na'urori, domin ba a samu dawo da dukkan na'urorin BVAS da aka yi amfani da su a babban zaɓen da ya gabata ba."

Source: Twitter
INEC za ta gwada tsarin zaɓe kafin 2027
Ya ƙara da cewa INEC na shirin gudanar da gwajin zaɓen shugaban ƙasa domin tabbatar da ingancin tsarin fasahar da za a yi amfani da shi, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
A cewarsa, wannan mataki zai taimaka wajen kauce wa matsalolin fasaha irin waɗanda suka shafi tsarin IReV a lokacin zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Hukumar INEC na shirin soke rijistar NDC
A wani labarin, kun ji cewa hukumar INEC ta ce za ta sake duba matsayin NDC bayan wata babbar kotun jiha ta soke hukuncin da ya tilasta mata yi wa jam’iyyar rajista.
Kwamishinan INEC kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu zabe, Mohammed Kudu Haruna, ya ce hukumar ta nemi kwafin hukuncin da aka tabbatar (CTC).
Ya kara da cewa kafin hukuncin ranar 10 ga Disambar 2025, INEC ta ayyana cewa ba za ta amince da bukatar NDC na yi mata rajista matsayin jam’iyyar siyasa ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng