PDP baza taba dawowa kan mulki ba a Najeriya - Tinubu
- Tsohon gwamnan jihar Legas kuma shugaban jam’iyyar APC Bola Tinubu ya soki babbar jam’iyyar, yace bazata taba komawa kan mulki ba
- Tinubu yayi maganar ne, a lokacin da yake jawabi a wurin taronsa na 10, wanda aka gudanar don murnar shigarsa shekara 66
- Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da cewa, kadasu saurari hakurin da jam’iyyar ta PDP ta bayar a farkon satin nan
Tsohon gwamnan jihar Legas kuma shugaban jam’iyyar APC Bola Tinubu ya soki babbar jam’iyyar, yace bazata taba komawa kan mulki ba.
Tinubu yayi maganar ne, a lokacin da yake jawabi a wurin tarosa na 10, wanda aka gudanar don murnar shigarsa shekara 66.
Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da cewa, kadasu saurari hakurin da jam’iyyar ta PDP ta bayar a farkon satin nan.
Ya kara da cewa jam’iyyar ta APC zata cigaba da fadakar da ‘yan Najeriya akan yanda jam’iyyar ta lalata arzikin kasar a lokacin mulkinta na shekaru 16 da tayi.
Tinubu yayi jawabi akan tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, akan wasikar da ya rubutawa shugaban kasa ta nuna gazawarsa, ya bayyana wannan wasikar a matsayin ta nuna “bakin ciki”, amma zai mayar masa da murtani wani lokacin.
A jawabin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana Tinubu a matsayin gwarzon dan siyasa wanda ya tallafawa mutane da dama, kuma mai son cigaban Najeriya da ma Afirika baki daya.
Mataimakin Shugaban kasa FarfesaYemi Osinbajo a jawabinsa, yace yayi murna da horon da ya samu tafannin aikin gwamnatin a lokacin da Tinubu yake Gwamnan jihar Legas, yace, a wannan lokaci ne akayi shimfidar wannan cigaba da ake gani a yanzu a jihar.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng