An kama ‘yan kungiyar Boko Haram da aka dade an nema tare da wasu mutane uku (hoto)

An kama ‘yan kungiyar Boko Haram da aka dade an nema tare da wasu mutane uku (hoto)

- Daya daga cikin ‘yan Boko Haram din da aka kama mai sanye da farar riga shine na 5 a cikin jerin sunayen wadanda Hukumar Sojoji Najeriya ke nema

- An kama wadanda ake zargin ‘yan Boko Haram tare da mutanen uku ‘yan kato da gora lokacin da suke tafiya a hanyar Kano

- Lokacin bincike da aka gudanar daya daga cikin ‘Yan Kato da Gora yayi ikirarin cewa sun kamo wadancan ne a jihar Legas

Daya daga cikin ‘yan Boko Haram din da aka kama mai sanye da farar riga shine na 5 a cikin jerin sunayen wadanda Hukumar Sojoji Najeriya, masu lakabin Operation Lafiya Dole ke nema.

An kama wadanda ake zargin ‘yan Boko Haram tare da mutanen uku ‘Yan Kato da Gora lokacin da suke tafiya a hanyar Kano-Azare road, a ranar Alhamis 29 ga watan Maris, 2018, a jihar Bauchi.

An kama ‘yan kungiyar Boko Haram da aka dade an nema tare da wasu mutane uku
An kama ‘yan kungiyar Boko Haram da aka dade an nema tare da wasu mutane uku

Lokacin da aka bincike da aka gudanar daya daga cikin ‘Yan Kato da Gora yayi ikirarin cewa sun kamo wadancan ne a jihar Legas, zaya kaisu ne ga hukumar ‘Yan Sanda masu Farin kaya a Maiduguri don cigaba da bincikarsu.

KU KARANTA KUMA: Mataimakin shugaban masu rinjaye a Majalisar Wakilai Buba Jibril ya mutu

Kokarin samun hukumar ‘Yan Sandan masu farin kaya don tabbatar da ikirarin ‘Yan Kato da Gorar. Bayan haka jami’an tsaro sun cigaba da bincike a manyan hanyoyi don cigaba da kama ‘yan kungiyar Boko Haram masu kokarin guduwa daga yankin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng