Manyan jami’an tsaro na kasa sun gano kullin da akeyi na lalata zaben 2019 - Fadar shugaban kasa
- Shuwagabannin tsaro na kasa sun bayyana cewa sun gano kulle kullen da wasu kungiyoyi keyi na kawo matsala a zaben mai zuwa
- Malam Garba Shehu ya bayyana haka a taron da aka gudanar na masu ruwa da tsaki da fannin hanyoyin sadarwa
- Lawal Daura a matsayinsa na Daraktan jami’an tsaro masu farin kaya, na daya daga cikin wadanda sukayi jawabi game da lamarin
Shuwagabannin tsaro na kasa sun bayyana cewa sun gano kulle kullen da wasu kungiyoyi keyi na kawo matsala a zaben mai zuwa na shekarar 2019.
Babban mai taimakawa shugaban kasa ta fannin hanyoyin sadarwa da hurdodin jama’a, Malam Garba Shehu ya bayyana hakan game da shuwagabannin tsaro a taron da aka gudanar, a jiya, na masu ruwa da tsaki da fannin hanyoyin sadarwa, a birnin tarayya.
Lawal Daura a matsayinsa na Daraktan jami’an tsaro masu farin kaya, na daya daga cikin wadanda sukayi jawabi game da lamarin; Daraktar Janar na masu bincike, Ambasada Ahmed Rufa’I Abubakar; Babban Jami’in Tsaro Janar Gabriel Olonisakin.
Shehu yayi gargadi ga kafafofin yada labarai akan al’amuran kungiyoyi masu zaman kansu da mazauna kasashen waje akan yin amfani dasu wurin yada maganganu da zasu kawo cikas a kokarin da akeyi na kawo karshe rashin zaman tsaro a Najeriya da kuma kumar zabe mai zaman kanta (INEC).
KU KARANTA KUMA: 2019: Ya kamata Shugaba Buhari ya zarce Inji Shugaban YSFON
Yace shuwagabannin tsaron sunce “Lamarin tsaro a kasar nan bai lalace ba kamar yanda kafofin labarai ke nunawa ba”.
Ya kuma bukaci kafofin labaran da su rage zuzuta labaran da suke dauka, saboda hakan zai rage wadannan matsaloli na kasar nan.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng