Babbar Magana: Ndume Ya Gano Matsalar da Tinubu ke Fuskanta a Fadar Shugaban Kasa
- Sanata Muhmmad Ali Ndume ya ce babbar matsalar gwamnatin Bola Tinubu ita ce mutanen da ke kewaye da shugaban kasa
- Ndume ya bayyana cewa ya rubuta wa Shugaba Tinubu wasiƙu biyu domin tattauna batutuwan tsaro da walwalar jama'a
- Ya ce har yanzu yana goyon bayan gwamnatin APC duk da sukar da yake yi, yana mai cewa burinsa a dauki matakan da suka dace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Sanatan mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya sake sukar gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Sanata Ndume ya bayyana cewa ɗaya daga cikin manyan matsalolin gwamnatin Tinubu ita ce yadda mutanen da ke kewaye da shugaban kasar ba sa iya gaya masa gaskiya.

Source: Facebook
Ndume ya bayyana hakan ne yayin hira a shirin Daily Politics na tashar Trust TV, inda ya yi magana kan alakarsa da Tinubu, yunƙurin ganawa da shi da kuma damuwarsa kan harkokin mulki, tsaro da walwalar 'yan Najeriya.
Da aka tambaye shi ko zai iya fadar maganganun sukar gwamnati da yake yi idan ya samu damar ganawa da Tinubu, Ndume ya ce shugaban kasar ya riga ya san halinsa.
Sanatan ya bayyana cewa ya taba ganawa da Tinubu a hukumance, ciki har da wata ganawa da ta shafi batun kudaden bangaren lafiya.
Ndume ya turawa Tinubu wasiku
Ndume ya ce ya rubuta wa shugaban kasa wasiƙu biyu yana neman ganawa da shi domin tattaunawa kan muhimman matsalolin kasa.
Ya ce:
"Na rubuta wasiƙu biyu, inda na zayyana batutuwan da nake son tattaunawa da shi, musamman kan tsaro da walwalar jama'a. Wadannan su ne manyan ayyukan gwamnati."
Sanatan ya yi nuni da cewa da yiwuwar wasu mutane da ke cikin fadar shugaban kasa ne suka hana shi samun damar ganawa da Tinubu.
Babbar matsalar da Tinubu ke fuskanta
Duk da cewa ya bayyana kansa a matsayin cikakken dan jam'iyyar APC, Ndume ya ce matsalar gwamnatin Tinubu tana tare xa mutanen da ke kusa da shugaban kasa.
Ya ce:
"Na taba fada a baya cewa matsalar shugaban kasa ita ce mutanen da ke kewaye da shi."
Ndume ya ce yawancin mutanen da ke kusa da Tinubu sun dade suna karkashinsa tun kafin ya zama shugaban kasa.

Source: Facebook
A rahoton Leadership, Ndume ya ci gaba da cewa:
"Kashi 95 cikin 100 na mutanen da ke kusa da shi masu dogaro da shi ne. Tun kafin ya zama shugaban kasa yana kula da su."
Ya ce wannan ne ya sa ba sa iya kallon shugaban kasa a ido su gaya masa cewa wata manufa da ya dauka ba zai haifar da sakamako mai kyau ba.
"Wannan na daga cikin matsalolin gwamnatinsa. Idan mutanen da ke kewaye da kai masu dogaro da kai ne, ba za su iya gaya maka cewa, 'Malam Shugaban kasa, wannan ba zai yi aiki ba," in ji shi.
Ndume ya hango karshen matsalar tsaro
A baya, kun ji cewa Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa Najeriya na da damar kawo ƙarshen matsalar tsaro cikin watanni shida kacal idan gwamnatin tarayya da gaske take.
Sanatan ya nuna damuwa kan yadda hare-hare ke ƙaruwa a yankin da ya fito watau Arewa maso Gabas da sauran sassan ƙasar nan.
A cewarsa, kawo ƙarshen rashin tsaro ba wai magana ce kawai ba, sai an nuna jajircewa wajen horas da sojoji, samar musu da kayan aiki, makamai da kuma ƙarfafa musu gwiwa.
Asali: Legit.ng

