Ya kamata a hukunta Danjuma - Inji kungiyar shari’a

Ya kamata a hukunta Danjuma - Inji kungiyar shari’a

- Babbar kungiyar shari’a ta bukaci gwamnatin tarayya data hukunta TY Danjuma, bisa ga babban laifin daya aikata

- Kungiyar fadi hakane bisa ga jawabin da yayi a taron yaye dalibai a jami’a jihar Taraba

- Tsoho Janar din ya bukaci ‘yan Najeriya dasu kare kansu daga ‘yan ta’adda, inda yace jami’an tsaro suna nuna son kai a ayyukansu na kare kasa daga hare-hare

Babbar kungiyar shari’a ta bukaci gwamnatin tarayya data hukunta TY Danjuma, bisa ga babban laifin daya aikata. Kungiyar fadi hakane bisa ga jawabin da yayi a taron yaye dalibai a jami’a jihar Taraba.

Tsoho Janar din ya bukaci ‘yan Najeriya dasu kare kansu daga ‘yan ta’adda, inda yace jami’an tsaro suna nuna son kai, ta fannin ayyukan da suke gudanarwa na kare kasa daga hare-hare. Kungiyar ta kalli jawabin Danjuma a matsayin abun Allah wadarai.

A wani jawabi da a

"kayi ranar Talata, Yusuf Rigachikun, Ciyaman na kungiyar ta jihar Kaduna, sun tambara jawabin na Danjuma a matsayin abun kunya daga tsohon Janar na Soja.

Yace: “A wani kira da TY Danjuma yayi akan mutanen kasa su dauki makamai su kare kansu da kuma zargin da yayi na cewa Sojaji Najeriya na sanya hannu wurin kisan mutane abun haushi ne.

“Bai dace ba ace mutum mai matsayi ya fito yana fadawa jama’a su dauki makamai saboda rashin gudanar da aiki yanda ya kamata da Sojoji keyi, yana kira ne ga rashin zaman lafiya, da tashin hankali, da cin amanar kasar wanda laifi ne babba."

KU KARANTA KUMA: Hukumar Hisbah na Kano ta kama almajirai 105 da suke keta dokar hana bara

Kungiyar tayi kira ga gwamnatin tarayya datayi bincike kuma ta hukunta janar din, akan wadannan maganganu da yayi a gabadar yara dalibai, wadanda a sansu dasauki juyawa tinani saboda yarinta. Hakan na nuna hari ne ga zaman lafiyar a kasa.

"Hukunta Janar din zai magance irin wadannan magananu daga mutane na bata zaman lafiya a Najeriya”.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng