Gwamna Abba Ya Raba wa Hadimai Filaye da Kudi, Ya Yi Magana kan Zaben Tinubu a 2027

Gwamna Abba Ya Raba wa Hadimai Filaye da Kudi, Ya Yi Magana kan Zaben Tinubu a 2027

  • Gwamna jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya jaddada goyon bayansa ga tazarcen shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027
  • Abba Gida Gida ya bayyana cewa jam'iyyar APC reshen jihar Kano za ta yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da nassra a kowane mataki
  • ya ce Kano za ta yi aiki domin APC ta yi nasara a zaɓen 2027
  • Gwamnan ya ce sake zaɓen Shugaba Tinubu da yi masa kamfe a lungu da sako nauyi ne da ya rataya a wuyan dukkan mambobin jam'iyyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Gwamnan Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa gwamnatin Kano za ta yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da ganin jam'iyyarsa ta APC ta samu gagarumar nasara a kowane mataki a zaben 2027.

Gwamnan ya kuma buƙaci duk masu riƙe da muƙaman siyasa a gwamnatinsa su shiga sahun masu yaɗa jam'iyyar tare da ƙarfafa shirinta a faɗin jihar.

Kara karanta wannan

Zaben gwamna: 'Yan daba sun buɗe wa mutane wuta, sun harbi wani jigon APC a Osun

Gwamna Abba.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf yana jawabi a taron rabawa magoya bayansa babura a gidan gwamnati Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Daily Trust ta rahoto cewa Abba ya bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa da aka gudanar da zaɓaɓɓun shugabanni da masu muƙaman gwamnati a gidan gwamnatin Kano.

Gwamnatin Kano na tare da Bola Tinubu

A cewar sanarwar da kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, Abba ya ce zai jagoranci tallata Tinubu ta yadda Kano za ta shiga gaba wajen nasarar shugaban a zabe mai zuwa.

Ya ce gwamnatinsa ba ta da wata nadama kan goyon bayan Tinubu, yana mai jan kunnen daukacin jami'an gwamnati da su kasance masu hadin kai da jajircewa wajen gudanar da ayyukan da za su gabbatar da nasarar APC.

Haka kuma, ya bukaci duk wani jami'i da ke aiki a karkashin gwamnatinsa da ya tabbatar yana tafiya kafada-da-kafada da tsare-tsaren jam'iyya mai mulki musamman batun rijistar zama dan APC.

Abba ya raba wa hadimansa filaye

Kara karanta wannan

Akwai matsala: Har yanzu ba a bai wa hukumar INEC kuɗin shirya babban zaben 2027 ba

Domin karfafa gwiwar ma'aikata da masu rike da mukaman siyasa, Gwamna Abba Yusuf ya amince da rabon filaye ga hadimansa sama da 300.

Wadanda za su amfana da wannan tsari sun hada da:

* Manyan Mataimaka na Musamman (SSA)

* Mataimaka na Musamman (SA)

* Manyan Masu Dauko Rahoto na Musamman

* Masu Dauko Rahoto na Musamman da Mataimaka na Kai da Kai (PA)

Baya ga filayen, Abba Gida-Gida ya kuma amince da ba kowane jami'i cikin wadanda aka ambata kyautar tsabar kudi Naira 100,000 domin rage musu radadin kalubalen tattalin arziki.

Abba da Tinubu.
Gwamna Abba Kabir Yusuf tare da Shugaba Bola Ahmed Tinubu lokacin da ya kai masa ziyara a Aso Rock Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

APC ta ce ta shirya tunkarar 2027

Da yake jawabi a taron, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Rt. Hon. Ismail Falgore, ya bayyana cewa za su ci gaba da tallata ayyukan alheri da ayyukan raya kasa da gwamnatin jihar ke gudanarwa.

Ya ce za su dage wajen bayyana wa jama'a ayyukan alherin Gwamna Abba. omin kara samun karbuwa da goyon bayan al'umma gabanin zaben 2027.

Abba ya yi garambawul a gwamnati

A baya, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi sauye-sauyen masu ba shi shawara.domin inganta aiki a gwamnatin jihar Kano.

Kara karanta wannan

Da gaske tsohon gwamna ya mutu a Najeriya? Gwamnatin Delta ta tsage gaskiya

Haka kuma gwamnan ya amince da waɗansu sababbin nade-naden domin karfafa tsarin mulki da inganta ayyukan gwamnati.

Abba Kabir ya amince da nada Bello Nuhu Bello a matsayin mai ba da shawara kan harkokin gudanarwa a ofishin gwamna.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262