Labari mai dadi: Buhari ya kaddamar da shirin wadatar da abinci

Labari mai dadi: Buhari ya kaddamar da shirin wadatar da abinci

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da shirin samar da isasshen abinci masu gina jiki.

Shugaban kasar ne da kansa zai jagoranci wannan shiri ba tare da taimakon kowa ba.

Mambobin wannan shiri sun hada da gwamnonin jihohin Kebbi, Taraba, Filato, Legas, Ebonyi, da kuma Delta.

Akwai kuma wakilan ministoci da ma'aikatun gwamnati masu ruwa da tsaki a lamarin.

Sai dai da babu wakilan manoma da makiyaya a majalisar.

Labari mai dadi: Buhari ya kaddamar da shirin wadatar da abinci
Labari mai dadi: Buhari ya kaddamar da shirin wadatar da abinci

Gwamnatin tarayyar ta ce wadannan bangarori biyu suna da damar da za su mika bayanan damuwarsu da shawarwarinsu ga majalisar.

KU KARANTA KUMA: Hukumar ‘yan sanda na binciken jami’an Civil Defense bisa kisan matashi a kan satar mangwaro

Sabuwar majalisar za ta kula da batutuwan da suka shafi wadata Najeriya da kayayyakin abinci.

A halin yanzu, bayan amincewan majalisar zantarwan tarayya FEC, shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan takardu biyu.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana wannan ne inda yace shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan takardan yarjejeniya tsakanin gwamnatin Najeriya, gwamnatin kasar Switzerland da kungiyar dawo da kudaden sata domin dawo da kudaden Najeriya da wasu yan Najeriya suka kai kasar Switzerland.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng