Me yayi zafi: Jami’ar Ibadan zata kori dalibai 328

Me yayi zafi: Jami’ar Ibadan zata kori dalibai 328

- Jami’ar Ibadan ta shirya korar dalibai 328 wadanda ke shekara ta farko, bisa 'sakamakon kunyatarwa da suka samu a jarabawa'

- Shugaban jami’ar, Idowu Olayinka, a jawabinsa ya yi zargin cewa hakan ya faru ne sakamakon rashin gudanar da jarabawar gwajin shiga jami’a ga daliban

- Olayinka yace, daliban basu samu abunda ake bukata ba, wanda hukumar zartarwa ta jami’ar ta yanke akan daliban

Jami’ar Ibadan, ta shirya korar dalibai 328, wadanda ke aji daya a jami’ar, bisa “sakamakon kunyatarwa da suka samu a jarabawa”, ta shekarar 2016/2017, shugaban makarantar ya bayyana haka, yace jami’ar ta kamala sunayen daliban da abun ya shafa a taron da suka gudanar a ranar 19 da 20 ga watan Maris, na sakamakon daliban na shekara 2016/2017.

Shugaban jami’ar, Idowu Olayinka, a jawabinsa ya zargi cewa hakan ya faru ne sakamakon rashin gudanar da jarabawar gwajin shiga jami’a ga daliban Post-UTME.

Yace, daya cikin tara na daliban basu samu abunda ake bukata ba na shiga ajin gaba.

Olayinka yace, “Idan aka lura, za’aga cewa summan daliban dake bangaren kimiyya, basuyi abun kirki ba jarabawarsu, wanda mafi karanci na maki da ake bukata shine 67.5%, na bangaren karatun Likitancin Dabbobi.

"Har gara ma bangaren karatun hurdodin dan Adam, sunfi samun sakamako mai kyau, wanda mafic in jarabawar sune bangaren karatun shari’a, da suka samu 99.2%."

KU KARANTA KUMA: Allah ya isa ga masu amfani da sunana a shafukan yanar gizo suna bata mun suna - Maryam Booth

Ya bukaci, a gyara al’amuran makarantar don inganta karatun daliban jami’ar tinda har sababbin daliban da aka dauka a shekarar 2017/2018, sune suka zauna jarabawar kuma suka kuma samu nasara akan jarabawar ta Post-UTME.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng