Ku daina buga kwalayen siyasa da hotunan Buhari – BCO ta gargadi yan siyasa

Ku daina buga kwalayen siyasa da hotunan Buhari – BCO ta gargadi yan siyasa

- Wata kungiyar masoyan Buhari ta bukaci yan siyasa das u daina buga kwalayen siyasa da hotunan shugaban kasa Buhari

- Sun ce masu jefa kuri’u zasuyi tunanin halayensu daya

- Kungiyar tace kowa tashi ta fisshe shi domin bazaar yaudari mutane da wannan yunkuri ba

Kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa Buhari ta kasa (BCO) ta yi kira ga yan siyasa da su daina buga kwalayen siyasa dauke da fuskar shugaban kasa Muhammadu Buhari a kwalayen yakin neman zabensu.

Daily Trust ta ruwaito cewa Alhaji Danlafi Garba Pasali yace masu hada hotunan Buhari da fuskokin sauran yan siyasa ba daidai bane.

Ku daina buga kwalayen siyasa da hotunan Buhari – BCO ta gargadi yan siyasa

Ku daina buga kwalayen siyasa da hotunan Buhari – BCO ta gargadi yan siyasa

Ya ce hakan zai sa ayi tunanin cewa halayen yan siyasan daya ne da na shugaban kasar.

KU KARANTA KUMA: Yan Shia 10,000 sun mamaye majalisar dokoki, sunce a shirye suke su mutu domin El-Zakzaky

A halin da ake ciki, kungiyar nasarar Buhari ta bayyana cewa tana kokarin hada ma shugaban kasa Muhammadu Buhari masoya miliyan biyar kafin zaben 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel