Saraki da Oyegun basu halarci taron karramawa ga Tinubu na goma ba
- Shugaban Majalisar Dattijai Bukola Saraki da John Oyegun, Ciyaman na jam’iyyar APC na tarayya, basu haralci taron karramawa ga Tinubu na goma ba
- Daga Saraki har Oyegun ba wanda yayi wani jawabi na taya murna ga Tinubu game da cikarsa shekara 66
- Yakubu Dogara shugaban majalisar wakilai, duk da bai samu halarta ba amma ya fadi sakon taya murnarsa a ranar Laraba
Shugaban Majalisar Dattijai Bukola Saraki da John Oyegun, Ciyaman na jam’iyyar APC na tarayya, basu haralci taron karramawa ga Tinubu na goma ba, wanda aka gabatar a Eko Convention Centre, a jihar Legas.
Daga Saraki har Oyegun ba wanda yayi wani jawabi na taya murna ga Tinubu game da cikarsa shekara 66, amma dai shugaban majalisar Saraki ya turawa Tinubu sakon taya murna ta kafar sadarwa na Tuwita, a ranar Alhamis da misalign karfe 7 na safe.
Yakubu Dogara shugaban majalisar wakilai, duk da bai samu halarta ba amma ya fadi sakon taya murnarsa a ranar Laraba.
KU KARANTA KUMA: An kama ‘yan kungiyar Boko Haram da aka dade an nema tare da wasu mutane uku
Labarai sun bazu akan cewa Tinubu na daya daga cikin wadanda suka bawa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara akan ya juya baya ga Karin wa’adi ga shuwagannin jam’iyyar APC wanda Oyegun ke jagoranta.
Duk da shawarar Saraki ta juya baya ga shugabancin jam’iyya, amma dayawa cikin Sanatoci, da Gwamnoni, da makarraban shugaban kasa sun halarci taron.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng