Aisha Musa
9376 articles published since 09 Agu 2016
9376 articles published since 09 Agu 2016
Rundunar sojin sun gano hakan ne yayin da suke tambayoyi ga babban Kwamandan Boko Haram mai suna Malu-Mamman Barde, wanda aka bibiyaa aka kuma kama a kudancin yankin Rann dake karamar hukumar Kala-Balge dake Borno.
Babban kotun tarayya dake Abuja tace lallai sai sufeto janar na yan sanda ya kama shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu sannan ya gabatar da shi a kotu a ranar 16 ga watan Agusta.
Shugaban kasar Najeriya na iya kasancewa da tarin makiya da mutanen dake sauraron ganin an tsige shi daga fadar shugaban kasa amma duk da haka yana da mabiya da yawa da suke ganinsa a matsayin abu mafi inganci da ya taba samun su.
Miss Belko wacce ta zamo abun so ga mutane, ta ja hankalin gwamnatin jihar Kebbi yayinda ta yanke shawarar daukar nauyin ci gaba da karatunta zuwa kowani maaranta da take so. Sn wallafa wannan labari ne a shafinsu na twitter.
Tsohon gwamnan wanda yayi murabus daga matsayinsa kuma ya sauya sheka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) yayi bayanin cewa ya bar matsayinsa ne saboda banbacin ra’ayi da aka kasa sasantawaa tsakaninsa da gwamnan jihar.
Ambasada James Barka, tsohon mukaddashin gwamnan jihar Adamawa kuma makusancin Gwamna Umaru Jibrilla ya bar jam’iyyar APC mai mulki. Barka yayinda yake sanar da ficewarsa daga APC ya kuma warware kullinsa da gwamnan jihar.
Rundunar yan sandan jihar Niger sun gurfanar da wani Yusuf Duguri mai shekaru 26 da Abubakar Adamu mai shekaru 45 dukkaninsu daga yankin Gedi-Gedi na Zaria Road, jihar Kano, bisa zargin satar mota, bayan sun wanki wani.
Shahararriyar jarumar da tauraronta ya daina haskawa a Kannywood, Zainab Abdullahi wacce aka fi sani da Zainab Indomie ta bayyana cewa ba ta san yadda aka yi rayuwar jarumtarta ta susuce ba duk da daukakar da ta samu a baya.
An rahoto cewa akalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu a wani hari da yan fashi suka kai Igarra, a karamar hukumar Akoko-Edo dake jihar Edo. Kwamishinan yan sanda, Mista Johnson Kokumo ya tabbatar da al’amarin ga manema labarai.
Aisha Musa
Samu kari